Makwabci ya harbe wani dalibi dan Najeriya har lahira kan kure sautin waka a Amurka

Makwabci ya harbe wani dalibi dan Najeriya har lahira kan kure sautin waka a Amurka

Wani dalibi dan Najeriya ya hadu da ajalinsa a hannun wani makwabcinsa da ya harbe shi har lahira bayan wani sabani ya shiga tsakaninsu kan kure sautin waka.

An harbe Oluwafemi Oyerinde mai shekara 18 a duniya, wanda ya kasance sabon shiga a jami'ar Kennesaw State University a Georgia, a wajen gidansa dake Stadium Village da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoba.

Ya kasance yana karantun injiniya sannan yana da burin shiga aikin soja.

Sashin yan sanda na yankin sun bayar da umurnin kama mutumin da aka zarga da kashe Oluwafemi Oyerinde a harabar gidan da ke Stadium Village.

Sashin yan sandan na CCPD na tuhumar Kashman Rael Thomas da laifin kisan kai da kuma wasu tuhume-tuhume biyu na cin zarafi.

An zargi Thomas da kashe Oyerinde mai shekara 18. Sannan kuma an raunata wasu biyu a wannan rana ta hanyar harbinsu, wato Khalil Bennett mai shekara 18 da kuma Jarius Bonner mai shekara 18

Daga bisani sai masu bincike suka gano damin tabar wiwi mai nauyin gram 159 a dakin Thomas bayan sun gudanar da bincike. Ana kuma tuhumar Thomas da mallakar tabar wiwi, a cewar AJC.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamnan Kogi: APC ta yi babban kamu na mambobin PDP har su 500

Kakakin jami'ar ta KSU, Tammy Demel ta tabbatar da lamarin a wani jawabi cewa Oyerinda ya kasance dalibin makarantar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng