Jerin Jihohin Najeriya da Suka Ba Alhazai Tallafin Kudin Aikin Hajji
- Gwamnonin jihohin Kano, Kebbi da Kogi sun bayar da tallafin kudin Hajji ga maniyyata a jihohinsu
- Matakin dai ya zama wajibi ne biyo bayan karin kudin da hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta yi wa alhazan kasar
- Da Legit Hausa ta zanta da Muhammad Aminu Kabir, wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum ya ce karyewar tattalin arziki ta shafi aikin Hajjin bana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
FCT, Abuja - Wasu gwamnonin jihohi sun ba da tallafin kudi ga alhazai domin taimaka musu wajen cikata kudaden aikin hajjin su biyo bayan karin kudin da NAHCON ta yi.
Wasu maniyyata a garin Jos na jihar Filato sun bukaci hukumar jin alhazan jihar da ta mayar musu da kudaden da suka ajiye na farko saboda karin kudin.
Jihohin Kano da Kebbi da dai sauransu sun ba da umarni tare da amincewa da biyan tallafin kudin aikin hajjin ga maniyyata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta tallafa da N90bn
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fitar da naira biliyan 90 domin tallafa wa maniyyata aikin hajjin 2024.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, majiya daga hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON) ta bayyana hakan a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.
Majiyar ta NAHCON ta ce wannan tallafin ya taimaka wajen hana maniyyata biya karin Naira miliyan 3.5, akalla a kan kudin da aka fara biya na Naira miliyan 4.9.
Wani babban jami'in fadar shugaban kasa ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin tarayya "ta biya wadannan makudan kudade domin ganin maniyyata sun sauke farali a bana."
Jihohin da suka bayar da tallafi:
Jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya amince da biyan karin N1.9m da aka yi wa maniyyata aikin hajji a jihar.
Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ahmed Idris, ya ce sama da mahajjata 4,875 ne ake sa ran za su tashi daga jihar don aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.
Jihar Kogi
Gwamna Ahmed Ododo na jihar Kogi ya biya sama da naira miliyan 800 domin a ba wa maniyyatan Kogi 460 izinin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024.
Ismaila Isah, mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai ya ce tuni hukumar alhazai ta jihar Kogi ta aiwatar da bukatar tallafin kudin.
Jihar Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya tallafawa maniyyata aikin Hajji da Naira biliyan 1.4.
Legit ta ruwaito cewa Yusuf ya amince da bayar da tallafin Naira 500,000 ga kowane mai zuwa hajji da ke jihar.
Jihar Osun
Gwamna Nurudeen Adeleke ya yi alkawarin yin duk abin da zai taimaka wajen gudanar da aikin hajji cikin sauki ga alhazan jihar.
Adeleke ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi bayan da aka aza harsashin gina sansanin alhazan jihar Osun a Osogbo.
Tattalin arziki ya shafi aikin Hajji
Da Legit Hausa ta zanta da Muhammad Aminu Kabir, wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum ya ce karyewar tattalin arziki ta shafi zuwa aikin Hajjin bana.
A cewarsa, tsadar da kujerun Hajji suka yi ba zai rasa nasaba da canjin Naira a kan Dala ba, da kuma tsadar man da jirage ke amfani da shi.
Muhammad Kabir ya ce:
"Dole ne mutane su yi korafi akan kudin aikin Hajji, domin idan aka duba shekarun baya, kudin bai kai N2m ba, amma yanzu ya haura N4m, dole mutane su yi korafi.
"Shawarar da za mu ba gwamnatin tarayya da na jihohi shi ne a dauki matakai na dawo da tattalin arzikin jama'a, ta yadda mutane za su samu kudin kai kansu aikin Hajji."
Haka zalika ya yi magana kan janye tallafin man fetur, wanda yake ganin shi ne babban dalilin durkusar da tattalin arzikin jama'ar kasar.
"A duba maganar kulle boda, a bude iyakokin kasar ta yadda Najeriya za ta samu wadatattun kayayyakin more rayuwa, sannan a tashi tsaye a yaki cin hanci da rashawa."
- A cewar Kabir.
Sanata Nduke ya caccaki NAHCOM
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda Sanata Ali Ndume ya dauki zafi kan karin kudin aikin Hajji da hukumar NAHCON ta yi a 2024.
Ndume ya ce ƙarin kuɗin ya tabbatar da rashin adalci hukumar karara, yana mai nuni da cewa da kyar mutane suka iya hada kudin farko da suka biya.
Asali: Legit.ng