Bayan Dala Ta Karye, Farashin Man Fetur Ya Ragu a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

Bayan Dala Ta Karye, Farashin Man Fetur Ya Ragu a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya musanta rahoton da ke yawo cewa farashin man fetur da dizal ya sauka a gidajen mai
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye, ya fitar ranar Laraba ya ce rahoton ƙarya ne gaba ɗayansa
  • Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su yi fatali da jita-jitar, inda ya ƙara da cewa NNPCL zai ci gaba da samar da isasshen mai a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kamfanin mai na Najeriya (NNPC Ltd) a ranar Laraba ya musanta rahotannin da ke yawo cewa cewa an samu raguwar farashin man fetur da man dizal.

NNPCL ya bayyana cewa rahotannin da ake yaɗawa cewa ya rage farashin man fetur da dizal a gidajen sayar da mai a fadin kasar nan ba gaskiya bane.

Kara karanta wannan

A wurin buɗa baki da manyan Malamai, Gwamnan APC ya rage farashin shinkafa da kashi 50

Mele Kyari da gidan man NNPCL.
NNPCL ya musanta saukar farashin fetur da dizal Hoto: NNPC Limited
Asali: Getty Images

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na manhajar X watau Twitter ranar Laraba, 27 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban sashin yaɗa labarai na NNPCl, Olufemi Soneye, wanda ya rattaba hannu kan sanarwar, ya ce rahotannin saukar farashin ba gaskiya bane.

Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa ƴan kasuwa sun rage farashin mai daga N640 zuwa N630 yayin da kamfanin NNPC ke sayar da lita kan N570 a gidajen mai.

Kamfanin NNPCL ya fayyace gaskiya

Amma da yake mayar da martani, kakakin NNPC, Mista Soneye ya ce rahotannin karya ne kuma ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da su gaba daya.

"Kamfanin NNPCL na son ya fayyace gaskiya game da jita-jitar da ke nuna cewa an rage farashin man fetur (PMS) da Automotive Gas Oil (dizal) a gidajen sayar da mai a fadin kasa.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da matar Gwamnan PDP bayan musayar wuta? Gaskiya ta bayyana

“Kamfani ya tabbatar da cewa waɗannan rahotanni karya ne kuma ya bukaci ɗaukacin ‘yan Najeriya da su yi watsi da su gaba daya."

- In ji Olufemi Soneye.

Kamfanin NNPC Ltd ya jaddada kudirinsa na ci gaba da samar da wadataccen man fetur a duk gidajen sayar da mai a lungu da saƙo na Najeriya.

Wakilinmu ya ziyarci wani gidan mai a yankin ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina kuma ya ganewa idonsa farashin da ake siyar fetur N700.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan da ke sayar da mai a gidan ya shaidawa Legit Hausa cewa babu wani ragi da aka samu a farashin litar fetur kwanan nan.

"A bakinka na fara ji, a ƴan kwanakin nan dai babu wani ragi kuma na san da akwai maganar manya za su sanar da mu, don haka ina ganin ba gaskiya bane," in ji shi.

Haka nan wani ɗan bunburutu da wakilinmu ya taras a wurin, Kabir Abdullahi, ya ce rabon da a samu ragin farashin mai tun wasu makonni da suka wuce.

Kara karanta wannan

Gidajen mai sun rage farashin fetur saboda matakin da NNPCL ya ɗauka, an samu bayani

Kabir wanda ake kira da Dogo ya ce ba zai iya tuna ainihin ranar ba, amma da N710 suke saye kwatsam lokaci guda kuma ya dawo N700.

Farashin Dala ya faɗo zuwa N1000?

Ƴan kasuwar canji sun musanta rahoton da ke yawo cewa farashin Dala ya ƙara karyewa, ya koma N1,000 kan kowace $1.

Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto ya karaɗe shafukan sada zumunta cewa Dala ta karye zuwa N1000 a Otal ɗin Sharaton da ke Zone 4 a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262