A Wurin Buɗa Baki da Manyan Malamai, Gwamnan APC Ya Rage Farashin Shinkafa da Kashi 50

A Wurin Buɗa Baki da Manyan Malamai, Gwamnan APC Ya Rage Farashin Shinkafa da Kashi 50

  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya rage kaso 50 cikin 100 a farashin shikafa domin ragewa al'ummar jihar wahalhalun tsadar rayuwa
  • Ya ce gwamnatinsa za ta sayar da buhunan shinkafa a rabin farashin kasuwa kuma za ta fara daga kan ma'aikatan gwamnati
  • Abiodun ya yi wannan furuci ne a wurin taron buɗa baki da ya shiryawa malamai a gidan gwamnati da ke Abeokuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara siyar da shinkafa ga al’ummar jihar a kan farashi mai rangwamen 50%.

Gwamna Abiodun ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin rage wa mazauna Ogun raɗaɗin tsadar rayuwar da ake ciki a ƙasar nan, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya faɗi Abu 1 da ya sa ƴan ta'adda suka daina kai hari makarantu a jiharsa

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun.
Gwamnatin Ogun ra rage farashin shinkafa da kaso 50 Hoto: Prince Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Ya ce gwamnatin za ta fara daga ma'aikata, inda ya ƙara da cewa burinsa kowa ya koma siyan kayan abinci kamar da kafin hauhawar farashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi wannan jawabi ne a lokacin buda baki na musamman da aka shirya wa kungiyar Limamai da Alfas ta jihar a fadar gwamnati da ke Abeokuta ranar Talata.

Meyasa gwamnan ya rage kaso 50%?

"Mun yanke shawarar fara sayar da shinkafa kuma za mu rage kashi 50% daga ainihin farashin da ake sayarwa. Za mu fara da ma’aikata, duk ma’aikatan gwamnati za su sayi shinkafa a rabin farashinta.
"Abin da muke ƙoƙarin yi shi ne sake mayar da al'umma matsayinsu na kafin hauhawar farashi, wannan ƙarfin da suke da shi na iya ɗaukar ɗawainiyar kansu muke son dawo masu da shi."

- Dapo Abiodun.

Gwamnan ya bayyana cewa an kafa kwamitin da zai kula da yadda za a sayar da kayayyakin ga mazauna jihar, a cewar TVC News.

Kara karanta wannan

Sojoji za su sako mutum 200 da aka kama bisa zargin ta'addanci, za a mayar da su jihar Arewa

Abiodun ya kara da cewa sayar da shinkafar da rangwamen kashi 50% na farashinta zai ba gwamnatinsa damar ci gaba da siyo wasu domin sayar wa jama’a.

Dala ba ta dawo N1000 ba

A wani rahoton kuma Ƴan kasuwar canji sun musanta rahoton da ke yawo cewa farashin Dala ya ƙara karyewa, ya koma N1,000 kan kowace $1.

Wannan na zuwa ne bayan wani rahoto ya karaɗe shafukan sada zumunta cewa Dala ta karye zuwa N1000 a Otal ɗin Sharaton da ke Zone 4 a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel