'Yan Bindiga Sun Kona Hedkwatar Karamar Hukuma, Sace Jami'an 'Yan Sanda a Wani Sabon Hari
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da mugayen makamai sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Anaocha ta jihar Anambra
- A yayin harin da suka kai cikin tsakar dare, miyagun sun ƙona ofishin ƴan sanda tare da hedkwatar ƙaramar hukumar
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayar da tabbacin cewa jami'an rundunar sun fatattaki ƴan bindigan daga baya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Wasu gungun ƴan bindiga kimanin 30 sun ƙona ofishin ƴan sanda na garin Neni da hedkwatar ƙaramar hukumar Anaocha a jihar Anambra.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 3:00 zuwa 4:00 na daren ranar Alhamis, 28 ga watan Maris 2024.
Ƴan bindigan dai sun kai wannan mummunan harin ne ɗauke da muggan makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu jami’an ƴan sanda ciki har da wata jami'ar ƴar sanda mace.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kai harin ne da bama-bamai da sauran abubuwan fashewa, rahoton gidan talabijin na Channels tv ya tabbatar.
Sai dai, ya musanta cewa sun yi awon gaba da jami'an ƴan sanda a yayin harin.
Ya ce an samu nasarar fatattakar ƴan ta’addan ne saboda ruwan wuta da jami'an ƴan sanda suka yi musu, wanda ya tilasta suka ranta a na kare.
Ƴan bindiga sun hallaka babban limami
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka babban limamin masallacin Juma'a na ƙauyen Keita da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun kai mummunan harin ne jim kaɗan bayan mutanen ƙauyen sun kammala sallar Isha'i.
Miyagun maharan sun kuma yi awon gaba da mutane masu yawa waɗanda ba a tantance adadin yawansu ba a yayin harin cikin har da mata.
Asali: Legit.ng