Babu Hannu Na a Kashe Sojojin Najeriya, Sarkin Delta da Ya Mika Kansa Ga ’Yan Sanda
- Ovie na masarautar Ewu-Urhobo, Mai Martaba Clement Oghenerukevwe Ikolo, Urhukpe 1, ya mika kansa ga ‘yan sanda
- Ikolo na daya daga cikin mutane takwas da hedikwatar tsaro (DHQ) ta ke nema ruwa a jallo dangane da kashe sojoji 17 a yankin Okuama
- Sarkin ya ce ya yanke shawarar mika kansa ga ‘yan sanda domin tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa ba shi da laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Asaba, jihar Delta - Ovie na masarautar Ewu-Urhobo, Mai Martaba Clement Oghenerukevwe Ikolo, Urhukpe 1, ya mika kansa ga ‘yan sandan jihar Delta.
Hedkwatar tsaro (DHQ) ta bayyana Ikolo a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin sa hannu a kashe sojoji 17 a yankin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu.
"Yan sanda na tsare da sarkin" - Edafe
An tattaro cewa basaraken ya kai kansa ga kwamishinan ‘yan sanda, Olufemi Abaniwonda da misalin karfe 6:41 na yammacin ranar Alhamis, 28 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bright Edafe, ya tabbatar da cewa rundunar tana tsare da sarkin, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Ikolo ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Delta da su kafa kwamitin bincike mai zaman kansa da zai binciki kashe sojoji.
Me yasa Sarkin Delta ya mika wuya?
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, sarkin ya bayyana cewa ya mika kansa ga hukuma ne domin tabbatar wa gwamnatin Najeriya da duniya cewa ba shi da hannu ko alaka da wadanda suka kashe sojojin.
An tattaro cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ne ya mika wa Ikolo sandar girma ta zama Ovie na masarautar Ewu-Urhobo a watan Nuwambar shekarar da ta gabata.
Ikolo dai yana zaune ne a birnin Landan kafin zabensa da aka yi da kuma nada shi sarautar Ovie bayan rasuwar tsohon sarkin kasar.
Tinubu ya karrama sojojin da aka kashe
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama sojojin Najeriya 17 da aka kashe a jihar Delta.
A yayin bikin binne sojojin, Bola Tinubu ya kuma dauki nauyin karatun 'ya'yan sojojin, tare da wasu alkawurra ga iyalansu.
Asali: Legit.ng