Babu sauran soyayya: Wata mata ta roki kotu ta raba auren su da mijinta

Babu sauran soyayya: Wata mata ta roki kotu ta raba auren su da mijinta

A ranar Larabar da ta gabata ne wata mata mai matsaikatan shekaru kuma uwar 'ya'ya biyar, Ajoke Badmus, ta roki wata kotun al'adu dake birnin Ibadan a jihar Oyo akan ta salwantar da auren dake tsakanin ta mijin ta, Badmus Moshood, inda ta ce babu abinda ya nufata sai ganin gawar ta.

Moshood, mijin wannan mata bai bayyana a gaban kotu ba har a karo biyu da ta gudanar da zamanta, wanda hakan ya sanya ya bar kotun babu wani zabi face raba auren dake tsakaninsu da mai dakinsa.

Babu sauran soyayya: Wata mata ta roki kotu ta raba auren su da mijinta
Babu sauran soyayya: Wata mata ta roki kotu ta raba auren su da mijinta

Sai dai 'ya'ya su na da zabin zama a wurin uwar su ko ubansu bayan sun mallaki hankullan kansu kamar yadda alkalin kotun Ademola Odunade ya shar'anta.

KARANTA KUMA: Yadda motsa jiki ke taimakawa wajen hana ta'ammali da sigari

Ajoke Badmus, wadda take ta mallakin shagon sayar da magunguna ta shaidawa kotun cewa, tun shekaru 25 da auren mijin na ta baya ko kulawa da sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng