Manyan Alkawura 4 da Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Iyalan Sojojin da Aka Kashe a Delta
- An yi jana'izar sojojin da aka yi wa kisan gilla a ƙauyen Okuama, jihar Delta a ranar Laraba, 27 ga watan Maris
- Shugaban ƙasa, hafsoshin tsaro, gwamnonin jihohi, da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci jana'izar wacce aka yi a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja
- Shugaba Tinubu ya ba sojojin lambar yabo ta ƙasa tare da sanar da bayar da tallafin karatu ga ƴaƴan jami'an tsaron da suka rasu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, 27 ga watan Maris, ya bi sahun hafsoshin tsaro, gwamnonin jihohi, da sauran manyan jami’an gwamnati domin yin bankwana da jami’an sojoji 17 da aka kashe a jihar Delta.
Shugaban ƙasan ya isa harabar maƙabartar ta ƙasa da misalin ƙarfe 4:08 na yamma. Bola Tinubu shi ne babban baƙo na musamman a wajen jana'izar.
A wajen jana’izar jami’an da aka yi a Abuja, shugaban ƙasan ya yi wasu muhimman alƙawura ga iyalan sojojin da aka kashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane alkawari Tinubu ya yi?
Ga alƙawuran da Tinubu ya yi wa iyalan sojojin da aka kashe kamar yadda Dada Olusegun, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan kafafen sada zumunta ya tabbatar a shafinsa na X.
1. Tinubu ya ba sojojin lambar yabo
A ranar Laraba ne shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga sojoji 17 da aka kashe a yankin Okuama na jihar Delta.
Manyan jami'ai huɗu daga cikinsu an ba su lambar yabo ta MON yayin da sauran sojoji 13 aka ba su lambar yabo ta MFR.
2. Gidaje ga iyalansu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da gidaje ga kowane daga cikin iyalan a duk inda suke so a faɗin ƙasar nan.
3. Tinubu ya ba ƴaƴansu tallafin karatu
Gwamnatin tarayya ta kuma ba ƴaƴan sojojin da suka rasu cikakken tallafin karatu har zuwa matakin jami’a ciki har da waɗanda ke ciki ba a haifa ba.
4. Gaggauta biyansu haƙƙoƙinsu
Shugaba Tinubu ya kuma umurci hukumar sojoji ta ƙasa da ta tabbatar an biya dukkan haƙƙoƙin sojojin da suka rasa ransu cikin kwanaki 90.
Tinubu ya ba dattawan Okuama umurni
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ba dattawan ƙauyen Okuama na jihar Delta umurni da su zakulo wadanda ake zargi da kisan.
Shugaban ƙasan ya kuma buƙace da su bada haɗin kai a binciken da ake yi domin gano miyagun da suka aikata wannan ɗanyen aikin.
Asali: Legit.ng