Tattalin Arziki: Darajar Naira Na Ƙara Zurarewa Ƙasa Yayin da $1 Ta Haura Zuwa N1,620

Tattalin Arziki: Darajar Naira Na Ƙara Zurarewa Ƙasa Yayin da $1 Ta Haura Zuwa N1,620

  • Darajar Naira a kasuwar hada-hadar kudi ta gwamnati da ta bayan fage na ci gaba da sunkuya wa ƙasa yayin da dala ke tashi sama
  • Tsakanin Talata da Laraba kawai, Naira ta fadi da N12.56, bayan an yi hada-hadarta a kan N1,603.38/$1 zuwa N1,615.94/$1
  • Masu shigo da kaya zuwa Najeriya na shan wahala wajen mallakar dalolin da suke bukata, wanda ya sa ake fargabar kudin kaya na iya karuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Darajar Naira ta sunkuya ƙasa zuwa N1,620 a kan kowacce $1 a kasuwar canji, sabanin yadda aka canja $1 kan N1,615 a ranar Talata.

Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa darajar kudin ƙasar ya sauka zuwa N1,615.94 a kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya (NAFEM).

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Tinubu na bada tallafin N500,000 ga matasa? Gaskiya ta bayyana

Farashin Naira akan dalar Amurka
Dala: Darajar Naira ta fadi zuwa N1,620/$1 a Najeriya. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Yadda aka yi cinikin Dala a makon nan

Wani rahoto da FMDQ ya fitar ya nuna cewa darajar Naira ta fadi daga N1,603.38/$1 zuwa N1,615.94/$1 a ranar Talata, kenan an samu faduwar N12.56.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darajar Naira sai da ta fadi warwas zuwa N1,635/$1 a kasuwar, amma daga bisani ta ƙara daraja zuwa N1,500/$1, inda aka samu bambancin N135.

Haka kuma, yawan dalar Amurka da aka yi hada-hadarta a ranar Talata ya haura da kaso 103.5% daga $122.18m zuwa $248.75, kenan an samu yawan cinikayya a ranar.

Akwai karancin dala a hannun 'yan kasuwa

Rahoton The Nation ya nuna cewa Naira na ci gaba da faduwa a kasuwannin hada-hada na gwamnati da na bayen fage sakamakon karancin dala a kasuwannin.

Masu shigo da kaya Najeriya na shan wahala wajen samun kuɗin da ake buƙata daga kasuwar FX ta gwamnati da ma kasuwar bayen fage.

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Wannan kuwa a mahangar masu sharhi kan tattali arziki, zai iya haifar da tsadar kayayyaki a kasar musamman wadanda ake shigowa da su daga waje.

Fabrairu/Maris: Dala ta tsaya waje daya

Idan muka yi la'akari da wani rahoto na Legit wanda ya nuna cewa an yi cinikin Naira kan 1,600/$1 ranar 15 ga watan Fabrairu, za mu iya cewa canjin dala zuwa Naira ya tsaya a waje daya ne.

A wancan watan, ana musayar Naira da dala akan farashin da ya kai N1,533/$1 zuwa N1,590/$1 a ranar Laraba a kasuwar bayan fage, inda har ta kai N1600/$1 a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel