Gwamnan Arewa Ya Faɗi Abu 1 da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Daina Kai Hari Makarantu a Jiharsa
- Gwamna Zulum ya bayyana dalilin da ya sa aka jima ba a ji ƴan ta'adda sun sace dalibai daga makarantu a jihar Borno ba
- Farfesa Babagana Zulum ya ce shirin samar da aminci a makarantu da suka kaddamar shekaru 7 zuwa 8 da suka wuce ya yi aiki yadda ya kamata
- Ya ce shirin ya gina katanga a mafi yawan makarantu kuma jami'an hukumomin tsaro na aiki tare domin tabbatar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Gwamnan Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa an kwana biyu ba a samu babban harin satar mutane musamman ɗaliban makaranta a jihar ba.
Farfesa Zulum ya ce hakan ta faru ne saboda shirin tabbatar da tsaro a makarantu na aikinsa yadda ya kamata a shekaru bakwai zuwa takwas da suka shuɗe.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin hira da masu ɗauko rahoton gidan gwamnati jim kaɗan bayan ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zulum ya faɗi matakan da suka ɗauka
Ya ce mafi akasarin makarantun jihar Borno an masu katanga kuma dakarun tsaro suna kewaye da makarantun domin tabbatar da tsaro, Daily Trust ta ruwaito.
Zulum ya ce baya ga yadda sojoji da sauran jami’an tsaro ke iya bakin ƙoƙarinsu, jihar Borno tana amfani da mafarauta, ‘yan banga da kuma jami'an JTF.
"Ba yanzu muka fara ba domin mun kaddamar da wannan shiri (Safe School Initiative) kimanin shekaru bakwai zuwa takwas da suka wuce saboda rashin tsaron da muke fama da shi a jihar mu.
"Ina da yaƙinin kusan duk makarantunmu suna da katanga a matsayin wani ɓangare na shirin. Mun kuma baza sojoji, ƴan JTF, mafarauta da ’yan banga suna aiki kafada-da-kafada don tabbatar da tsaro a makarantunmu.
"Saboda haka muna iya bakin ƙoƙarinmu, na san cewa kun rabu da jin harin satar ɗalibai a makarantu a jihar Borno, duk hakan ya faru ne saboda shirin mu na aiki yadda ya kamata.
- Babagana Zulum.
Gwamnan ya kuma yabawa rundunar sojoji, ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro bisa haɗin kan da suka ba shi wajen aiki tare domin tsare makarantu, rahoton Vanguard.
Sojoji sun wanke waɗanda ake zargi
A wani rahoton kuma Hukumar sojojin ƙasa ta Najeriya za ta saki kimanin mutum 200 da ta wanke daga zargin ta'addanci a Najeriya.
Kwamishinar harkokin mata da kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida ne ake sa ran za ta karɓi mutanen a madadin gwamnatin Borno.
Asali: Legit.ng