Sojoji Za Su Sako Mutum 200 da Aka Kama Bisa Zargin Ta'addanci, Za a Mayar da Su Jihar Arewa

Sojoji Za Su Sako Mutum 200 da Aka Kama Bisa Zargin Ta'addanci, Za a Mayar da Su Jihar Arewa

  • Hukumar sojojin ƙasa ta Najeriya za ta saki kimanin mutum 200 da ta wanke daga zargin ta'addanci a Najeriya
  • Rahoto ya nuna cewa za a miƙa mutanen ga gwamnatin jihar Borno ranar Talata, 26 ga watan Maris, 2024
  • Kwamishinar harkokin mata da kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida ne ake sa ran za ta karɓi mutanen a madadin gwamnatin Borno

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta shirya za ta saki sama da mutane 200 da aka wanke daga zargin alaƙa da ƙungiyar ƴan ta'addan Boko Haram.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, sojoji sun kama waɗannan mutanen ne a lokacin da ayyukan ƴan tada kayar baya ke cin kasuwa a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya shiga sabuwar matsala kan zargin alaƙa da ƴan bindiga, bayanai sun fito

Shugaban rundunar sojin ƙasa, Taoreed Lagbaja.
Za a sako mutum 200 da aka wanke daga zargin ta'addanci Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Bincike ya nuna cewa za a mika su ga gwamnatin jihar Borno domin su koma cikin al’umma yadda ya kamata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a miƙa su ga gwamnatin Zulum?

Za a gudanar da taron sakin mutanen a barikin sojojin Giwa da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno a safiyar ranar Talata, rahoton Nairaland.

"Jami'an tsaro sun wanke kimanin mutane 200 daga zargin alaƙa da Boko Haram da duk wani laifi kuma za a miƙa su ga gwamnatin Borno domin sake mayar da su cikin al'umma su ci gaba da rayuwa.
"An shirya bikin mika mutanen da aka wanke daga zargin a safiyar yau (Talata, 26 ga watan Maris) da karfe 10:00 na safe a barikin Giwa," in ji wata majiya.

Majiyar ta ce kwamishinar harkokin mata ta Borno, Zuwaira Gambo da takwaranta na yada labarai da tsaron cikin gida Farfesa Tar Umar za su karbi wadanda aka sako a madadin gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan PDP na dab da rasa kujerarsa yayin da CJ ya kafa kwamitin mutum 7

Gwamnati ta gurfanar da wani 'Blogger'

A wani rahoton kun ji cewa FG ta gurfanar da Chike Victor Ibezim a gaban kotu bisa zargin ɓata sunan tsohon ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola

Ibezim ya yi zargin cewa Fashola ne ya rubuta hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ya ba APC nasara

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel