Ana Tsaka da Shan Ruwa, 'Yan Bindiga Sun Kai Hari, Sun Sace Malamin Musulunci a Arewa
- Miyagu sun sake kai hari yankin Iyara da ke karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi inda suka sace malamin Musulunci, Quasim Musa
- Maharan sun yi garkuwa da babban limamin garin Iyara da ke jihar bayan sun yi ta harbe-harbe domin firgita mutanen yankin
- Lamarin ya faru ne bayan shan ruwa a daren jiya Litinin 25 ga watan Maris kamar yadda rundunar 'yan sanda ta tabbatar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Wasu 'yan bindiga sun sace fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya.
Maharan sun sace babban limamin ne na Iyara da ke karamar hukumar Ijumu a jihar mai suna Sheikh Quasim Musa.
Yaushe aka sace malamin Musuluncin Kogi?
Tribune ta tattaro cewa an sace Musa ne da daren jiya Litinin 25 ga watan Maris a garin Ilukpa da ke karamar hukumar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun birkita mutanen garin da harbe-harbe kafin su dauke malamin su tafi da shi.
Wani daga cikin iyalan malamin da ya bukaci a boye sunansa ya ce har zuwa yanzu ba su samu bayani daga maharan ba.
Majiyar ta ce:
"Ya ku 'yan yankin Iyara, rashin tsaro da ke samun kasar ya shafe mu a wannan yanki namu."
"A ranar 25 ga watan Maris, wasu 'yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun sace babban limamin Iyara, Sheikh Quasim Musa bayan harbe-harbe."
Al'ummar Kogi sun roki addu'a daga jama'a
Har ila yau, majiyar ta yi Allah wadai da harin musamman a wannan wata mai albarka na Ramadan, cewar Daily Post.
Ta bukaci jama'an yankin da su dage da addu'a domin ganin an ceto malamin daga hannun miyagun.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata 26 ga watan Maris.
Maharan sun farmaki dakunan daliban Jami'a
Kun ji cewa wasu mahara sun kai hari dakunan kwanan dalibai mata a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Lokaja a jihar Kogi.
Maharan sun raunata dalibai guda biyu tare da sace musu wayoyi da kudi da sarki yayin harin da suka shafe awa biyu su na yi.
Asali: Legit.ng