Shugaba Tinubu Zai Halarci Jana'izar Sojojin da Aka Kashe a Delta, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Zai Halarci Jana'izar Sojojin da Aka Kashe a Delta, Bayanai Sun Fito

  • Rahotanni sun ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci jana’izar sojoji 17 da aka kashe kwanan nan a jihar Delta
  • Wani rahoto ya tabbatar da cewa za a yi jana'izar ne a maƙabartar ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Laraba 27 ga watan Maris
  • Shugaban ƙasan zai halarci wurin a matsayin babban baƙo na musamman kuma zai taimaka wajen gudanar da jana'izar jaruman sojojin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Za a yi jana'izar sojojin Najeriya da suka rasa rayukansu a yankin Okuama na jihar Delta a ranar Laraba, 27 ga watan Maris 2024, a maƙabartar ƙasa da ke Abuja.

A cewar rahoton jaridar The Guardian, an shirya gudanar da jana'izar ne da ƙarfe 3:00 na rana.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya samo mafita kan hanyar kawo karshen 'yan bindiga a Arewacin Najeriya

Tinubu zai je jana'izar sojojin da aka kashe a Delta
Shugaba Tinubu zai halarci jana'izar ne a ranar Laraba, 26 ga watan Maris 2024. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu zai halarci jana'izar sojoji

A cewar wata majiya da ba a bayyana sunanta ba, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, babban kwamandan rundunar sojojin Najeriya, zai halarci jana'izar a matsayin babban baƙo na musamman, a cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu ruwa da tsaki da dama sun yi Allah-wadai da kisan sojojin, inda Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin cewa waɗanda suka aikata mummunan laifin za su fuskanci hukunci.

Legit Hausa ta rahoto cewa sojojin da suka rasu sun haɗa da manyan jami’ai huɗu a yankin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Da farko dai jami’an soji sun bayyana cewa an kashe su ne yayin wani aikin wanzar da zaman lafiya da nufin magance rikici tsakanin al’ummar Okuama da Okoloba.

Rahotanni daga jami’an soji sun bayyana cewa sojoji 16 ne suka rasa rayukansu, amma a halin yanzu rundunar ta bayyana sunayen sojoji 17 da suka mutu tare da hotunansu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun shiga daji sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Katsina

Kisan sojoji: Majalisa ta aika da saƙo ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan diyya ga iyalan sojoji 17 da aka kashe.

Majalisar ta kuma bada umarni ga kwamitocin sojojin ƙasa da na ruwa da na tsaro da su haɗa kai da hukumar sojin Najeriya domin gudanar da bincike kan kisan gillan da aka yi wa sojojin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng