Gidajen Mai Sun Rage Farashin Fetur Saboda Matakin da NNPCL Ya Ɗauka, an Samu Bayani
- Farashin litar fetur ya sauka a gidajen mai na jihar Enugu, sakamakon cika alkawarin da NNPLC ya fara yi wa ƴan kasuwar mai
- Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Talatar nan ana sayar da litar fetur akan N660 sabanin yadda aka sayar da litar a kan N720 a baya
- Wani ɗan kasuwar mai, Obinna Ndukwe ya ba da tabbacin cewa farashin fetur zai ci gaba da sauka ma damar NNPCL ta yi abin da ya dace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Enugu - Rahotanni na nuni da cewa wasu gidajen mai a jihar Enugu sun rage farashin fetur sakamakon wani mataki da NNPLC ya ɗauka.
Sabon farashin fetur a Enugu
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa yanzu gidajen mai a jihar na sayar da lita ɗaya a kan N660, wasu kuma a kan N680.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin wannan ranar ta Talata, gidajen man na sayar da lita a kan N690 zuwa N720, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Wani ɗan kasuwar mai, Mr. Obinna Ndukwe ya sanar da cewa kamfanin fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi wa ƴan kasuwa alkawarin ba su wadataccen mai, shi ne suka rage farashin.
"Farashin fetur zai kara faduwa" - Ndukwe
Ndukwe ya tabbatar da cewa tuni wasu daga cikin dillalan mai suka samu fetur ɗin a farashi mai rahusa daga NNPCL.
Ya yi alƙawarin cewa farashin fetur zai ci gaba da faɗuwa ƙasa ma damar NNPCL ya ci gaba da ba dillalai man a wadace.
“Zan iya danganta wannan faduwar farashin da alkawarin da NNPC ta yi wa ‘yan kasuwa cewa za wadata su da fetur din kuma a farashi mai sauki.
- In ji Ndukwe.
An gargadi gidajen mai masu matse lita
A baya gwamnatin jihar Enugu ta yi barazanar rufe gidajen mai da aka kama suna matse lita.
Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa akwai wasu gidajen mai da gwamnatin ke zargi suna matse lita domin zaluntar masu sayen fetur.
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Emeka Ajogwu ya yi wannan zargin ne a lokacin da ya kai ziyara wasu gidajen mai na kwaryar jihar.
Arahar fetur: Najeriya ta koma ƙasa ta 22
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa, Najeriya ta koma ƙasa ta 22 a jerin ƙasashen duniya da ke da arahar fetur a 2024.
A yayin da mafi yawan ƙasashe ke sayar da litar fetur a kan N1,500 ko sama da haka, Najeriya na sayar da nata a kan kimanin N660.25.
Asali: Legit.ng