Manyan Kwamandojin 'Yan Ta'adda 2 Sun Mika Wuya a Hannun Sojoji
- Wasu kwamandojin ƴan ta'addan Boko Haram sun nemi sauƙi, sun miƙa wuya ga dakarun sojoji a tafkin Chadi
- Ƴan ta'addan sun miƙa wuya ne ga dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF a jihar Borno
- Daraktan yaɗa labarai na rundunar MNJTF wanda ya tabbatar da hakan ya yi nuni da cewa an kuma samu makamai masu yawa a hannunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wasu kwamandojin ƴan ta'adda biyu sun miƙa wuya ga dakarun rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF a yankin tafkin Chadi.
Babban jami’in yaɗa labarai na rundunar MNJTF, Laftanal-Kanal Abubakar Abdullahi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar jaridar Leadership.
Abdullahi ya ce ƴan ta’addan biyu na ƙungiyar Boko Haram ne ɓangaren BaKoura Buduma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ƴan ta'addan suka miƙa wuya?
A cewar sanarwar ƴan ta'addan masu suna Ibrahim Muhammed da Auwal Muhammed, wanda aka fi sani da Wanka, sun miƙa wuya ne ga dakarun sashe na uku na rundunar a ranar Talata, 26 ga watan Maris, 2024.
Jaridar The Guardian ta ce kakakin na MNJTF ya danganta miƙa wuyan da suka yi kan yadda jami'an tsaro suka ƙara ƙaimi wajen kai musu hare-hare a maɓoyarsu.
A kalamansa:
"Mutanen biyu, kwamandojin da ke aiki a tsibiran tafkin Chadi, sun yanke shawarar miƙa wuya ne sakamakon matsin lamba daga ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi."
An samu makamai a hannunsu
A cewar sanarwar ƴan ta'addan a yayin binciken farko, sun tabbatar da cewa sun daɗe suna aikata ayyukan ta'addanci a ƙarƙashin ɓangaren Bakoura Baduma na ƙungiyar Boko Haram.
Sun bayyana cewa sun kwashe shekara 15 a cikin ƙungiyar inda suke gudanar da ayyukansu a Kwallaram da ke a tafkin Chadi.
Ya bayyana cewa makaman da aka samu a wajensu sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, jigida guda takwas, harsasai masu kaurin 7.62mm guda 191, gurneti guda biyu da rediyon hannu guda ɗaya.
Sojoji sun sheƙe ɗan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar sheƙe wani ɗsn ta'adda a jihar Sokoto.
Ɗan ta’addan ya sha yin shiga a matsayin ɗan sanda wajen yaudara da yin garkuwa da mutane masu yawa da ba a san adadinsu ba.
Asali: Legit.ng