Gwamnatin Tinubu Ta Gurfanar da Wani 'Blogger' a Kotu, Ta Jero Laifin da Ya Tafkawa Ministan Buhari

Gwamnatin Tinubu Ta Gurfanar da Wani 'Blogger' a Kotu, Ta Jero Laifin da Ya Tafkawa Ministan Buhari

  • An gurfanar da Chike Victor Ibezim a gaban kotu bisa zargin ɓata sunan tsohon ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola
  • Ibezim ya yi zargin cewa Fashola ne ya rubuta hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ya ba APC nasara
  • Ya gurfana gaban babbar kotun tarayya mai zama a birnin Abuja ranar Litinin, 25 ga watan Maris kan tuhume-tuhume shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta gurfanar da mawallafin yanar gizo, Chike Victor Ibezim a gaban kotu.

Gwamnatin ta gurfanar da mutumin ne bisa zargin ɓata sunan tsohon ministan ayyuka da gidaje a mulkin Muhammadu Buhari, Babatunde Raji Fashola.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

Ibezim da Fashola.
An maka mutumin da ya yi wa Fashola ƙage Hoto: @JustPhixical/Babatunde Raji Fashola
Asali: Twitter

Mista Ibezim ya gurfana gaban mai shari'a Bolaji Olajuwon na babban kotun tarayya mai zama a Abuja kan tuhume-tuhume shida ranar Litinin, 25 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifi mutumin ya aikata?

Kamar yadda Punch ta ruwaito, Ibezim da wasu mutum biyu sun yi iƙirarin cewa Fashola ne ya umurci kotun sauraron kararrakin zaben shugaban ƙasa ta ba APC nasara.

A cewarsu, tsohon ministan ne ya umarci kotun zaɓen ta bai wa APC da Tinubu nasara a kararrakin da jam'iyyun PDP da LP suka shigar kan zaben 2023.

Fashola ya mayar da martani

Sai dai tsohon gwamnan na Legas, ya fito ya yi watsi da zargin, yana mai bayyana shi a matsayin "mara tushe kuma karya."

Ya kuma ce wadanda ke da alhakin wannan zargi da aka rataya masa “suna ƙoƙarin tada zaune tsaye ne kawai."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya kori mutumin Buhari, ya naɗa sabon shugaban hukumar kula da kayan tarihi

Wannan laifin ne a karkashin sashe na 27(1) (b) na dokar hana aikata laifuka ta Intanet, dokar kariya 2015, da sauransu, in ji rahoton PM News.

Ɗaya daga cikin tuhumar da ake masa ta ce:

"Cewa kai Ibezim Chike Victor tare da Jackson Udeh, Nnamdi Emmanuel Ibezim da Reporters.ng (shafin yanar gizo) a ranar 5 ga watan Augusta, 2023 kuka haɗa baki kuka wallafa labarin ƙarya a shafinku na reportera.ng news kan Babatunde Raji Fashola."

Sai dai alkalin kotun, Bolaji Olajuwon, ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Afrilu domin ci gaba da shari’a.

CBN ya sayar da dala ga BDC

A wani rahoton kuma Babban bankin Najeriya ya ƙara karya dala yayin da ya siyar da $10,000 ga kowane ɗan canji kan farashin N1,251.

A wata sanarwa, CBN ya umarci dukkan ƴan canjin su ƙara kashi 1.5% kan farashin da aka siyar masu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel