Hajjin 2024: Alhazan Jihohi 3 Sun Nemi a Dawo Masu da Kuɗinsu Bayan Ƙarin N1.9m
- Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ce ta yanke N6.8m a matsayin kuɗin aikin hajjin bana 2024/1445H
- NAHCON ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin canjin Dala, inda ta umarci maniyyatan da suka biya N4.9m su cika N1.9m
- Tuni dai wasu maniyyata suka fara neman a dawo masu da kuɗin da suka biya na farko duk da NAHCON ta ce sabon maniyyaci zai biya N8.2m
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Mafi akasarin mutanen da suka yi niyyar sauke farali a bana 2024 sun fara zuwa hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi suna neman a dawo masu da kuɗaɗensu.
Hakan ya biyo bayan matakin da hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ɗauka na ƙara N1.9m a kan kowace kujerar hajji, kana ta umarci maniyyata su hanzarta biya.
Meyasa NAHCON ta kara kuɗin hajji?
A ranar Lahadi ne NAHCON ta kara kudin jigilar mahajjatan bana zuwa kasar Saudiyya da N1, 918,032.91 yayin da ta tsayar da wa'adin ranar 28 ga Maris, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Disamba, hukumar ta ƙayyade kuɗin zuwa hajji N4.9m kan kowace kujera ɗaya kuma ta ɗauki wannan matakin a lokacin ana canjin Dala a farashin N897.
Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata, hukumar ta bukaci wadanda suka biya kudin farko da su kara Naira miliyan 1.9, domin adadin ya kai Naira miliyan 6.8.
A wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yaɗa labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce an ɗauki wannan matakin ne saboda tashin Dala.
Maniyyata sun fara haƙura da hajjin bana
Wani bincike daga hukumomin jin daɗin alhazai na jihohin Arewa da Kudancin kasar nan ya nuna cewa mahajjata kalilan ne suka fara kokarin cika kuɗin.
Yayin da mafi yawa suka fara neman a dawo masu da kuɗaɗen da suka biya na farko domin ba zasu iya cika N1.9m, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A Kano, har yanzu maniyyata ba su san haƙiƙanin kuɗin kujerar hajjin bana ba yayin da hukumar jin daɗin alhazan Kano ta ce har yanzun ba su cimma matsaya ba.
Hukumar ta bayyana cewa daga nan zuwa awanni 24 masu zuwa, za su yanke hukunci kan wannam lamari na ƙarin kuɗin da aka samu, cewar The Cable.
A jihar Kwara kuwa wata majiya daga hukumar jin daɗin alhazai ta ce tuni maniyyata suka fara neman a mayar masu da kudinsu, sun ce ba zasu iya cika kuɗin ba.
"A yanzu da nake magana da ku, mutanen da ba su wuce 50 bane suka zo za su cika ragowar kuɗin yau, kuma kwana biyu kaɗai suka rage mana kowa ya kawo cikonsa," in ji majiyar.
Haka nan a jihar Legas, rahotanni sun nuna cewa mutane da yawa sun garzaya hukumar jin daɗin alhazai suna neman a ba su kuɗinsu, sun ce babu wani ƙari da za su yi.
"Wasu sun zo nan sun faɗa mana ba su da kuɗin da za su cika yayin da wasu kuma suka zo cika kuɗin, abin da ke faruwa kenan, muna da yau, gobe da jibi kafin a rufe,"
- A cewar wani jami'i.
Wata mata daga cikin maniyyatan jihar Katsina, Mariya Bello, ta shaidawa Legit Hausa cewa wannan ƙarin ka iya zama sanadin rashin zuwanta ƙasa mai tsarki a 2024.
Ta ce tun shekara biyu baya aka biya kuɗin kuma a bana ma sai da ƴaƴanta suka haɗa suka cika mata amma yanzun an sake samun ƙari.
"Ni na cire rai gaskiya amma na barwa Allah zaɓi, tun farko miji na ya biya kudin, daga baya Allah ya masa rasuwa, ƴaƴana suka ce ni zanje.
"A farko aka ce mu ƙara kuɗi, yaran nan suka haɗa kuɗi suka cika, yanzu kuma an sake cewa mu ƙara, ba wanda zan matsawa dole sai an cika kuɗin nan. Allah ya sa haka shi ne mafi alheri," in ji ta
Saudiyya ta hana Umrah sau 2 a Ramadan
A wani rahoton kuma Ƙasar Saudiyya ta sanar da kimtse damar alhazai na yin Umrah sau biyu ko fiye da haka a cikin watan Ramadana.
Wannan doka an kawo ta ne don rage cunkoson jama'a a lokacin watan Ramadana, watan da aka fi ganin masu Umrah a kasar mai tsarki duk shekara.
Asali: Legit.ng