El-Rufai Ya Rikita Komai Yayin da Yake Ganawa da Shugabannin APC da Jam’iyyun Adawa
- Yayin da ake ci gaba da yada jita-jitar cewa Nasir El-Rufai zai bar jam'iyyar APC, tsohon gwamnan ya sake wata ganawa a Abuja
- El-Rufai ya yi muhimmiyar ganawa da shugabannin jam'iyyar APC da kuma jam'iyyun adawa na PDP da SDP a birnin Abuja
- Hakan ya biyo bayan jita-jitar cewa tsohon gwamnan zai watsar da kashin jam'iyyar APC kan shirye-shiryen zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fara wata ganawa ta musamman da shugabannin jam'iyyar APC.
An gano tsohon gwamnan da shugabannin jam'iyyar APC da kuma na SDP a gidansa da ke birnin Abuja kamar yadda aka wallafa a shafin X.
Su waye suka gana da El-Rufai?
Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai Sanata Abubakar Gada da kuma shugaban jam'iyyar SDP, Shehu Musa Gabam da sauran jiga-jigan jam'iyyar, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da Sanata Teslim Folarin wanda ya yi takarar gwamnan jihar Oyo a zaben 2023 da jigon jam'iyyar PDP, Sanata Nazifi Suleiman daga jihar Bauchi.
Jita-jitar da ake yadawa kan El-Rufai
Wannan ganawa an yi ta ne a daren jiya Lahadi 24 ga watan Maris a gidan Sanata Gada da ke birnin Abuja, cewar rahoton Daily Post.
Wannan na zuwa ne bayan El-Rufai ya gana da shugabannin jam'iyyar APC ciki har da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.
Hakan ya biyo bayan jita-jitar da ake yi cewa tsohon gwamnan ya shirya barin jam'iyya mai mulki zuwa ta adawa a kasar.
Akwai yiwuwar El-Rufai ya hade da Obi
Kun ji cewa, Daniel Bwala, tsohon kakakin dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi hasashen makomar Nasir El-Rufai.
Bwala ya ce akwai yiwuwar tsohon gwamnan Kaduna ya hade da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi.
Wannan na zuwa ne yayin da ake jita-jitar El-Rufai da Obi dukkansu za su iya barin jam'iyyunsu kafin zaben 2027.
Asali: Legit.ng