Dattawan Arewa sun yi kakkausar magana kan satar yara ɗalibai
- Kungiyar dattawan Arewa ta yi kakkausar magana kan satar yara ɗalibai a yankin Arewa, tana mai cewa "ya isa haka"
- Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa, ya bayyana hakan a wata sanarwa ta hannun Abdul-Azeez Suleiman
- Dattawan Arewa sun kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa ya gargadi gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu da cewar "ya isa haka" kan satar yara ɗalibai a yankin.
Daliban Kuriga: Dattawan Arewa sun yi magana
Farfesa Abdullahi, a cewar wata sanarwa da daraktan watsa labarai na NEF, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, ya ce kungiyar ta yi murna da dawowar daliban makarantar Kuriga da aka sace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito sanarwar na cewa:
"A matsayinmu na dattawa, muna murna da dawowar yaran, sai dai muna ganin akwai bukatar a binciki lafiyar jiki da ƙwaƙwalwarsu yayin da za su shiga cikin jama'a.
"Yawaitar sace-sacen yara dalibai ya fara zama ruwan dare a Arewa, wanda ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan inganta tsaro a yankin."
"Gwamnatin Tinubu ta gaza" - Kungiyar Arewa
Kungiyar dattawan Arewa ta kuma ce:
"Kungiyar NEF na magana da kakkausar murya cewa 'ya isa haka', tsaro da lafiyar yaranmu ba abin da za a yi wasa da shi bane.
"Ba za mu ci gaba da lamuntar yadda ƴan Najeriya, musamman waɗanda ke a yankin Arewa ke rayuwa a cikin fargaba da rashin tsaro ba."
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa kungiyar NEF ta ce gwamnatin Tinubu ta gaza wajen samar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.
Dattawan Arewa sun yi kira ga gwamnatoci da masu ruwa da tsaki da su yi aiki kafada-da-kafada wajen ganin cewa yara suna zuwa makaranta ba tare da fargaba ba.
An ceto daliban Kuriga da aka sace
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa an kubutar da dalibai 137 da aka sace su a garin Kuriga da ke jihar Kaduna.
Daliban sun shafe tsawon kwanaki 16 a hannun masu garkuwa da mutane kafin suka samu ƴanci, kamar yadda gwamnatin Kaduna ta sanar.
Asali: Legit.ng