An Shiga Makoki Bayan Gobara Ta Cinye Wata Dalibar Jami’ar Tarayya da Ke Yobe

An Shiga Makoki Bayan Gobara Ta Cinye Wata Dalibar Jami’ar Tarayya da Ke Yobe

  • An bayyana yadda wata daliba ta rasa ranta bayan tashin gobara a jami'ar tarayya ta jihar Yobe, FUGA
  • Wannan mummunan lamari ya auku ne da sanyin safiyar ranar Asabar 23 ga watan Maris, inji rahoto
  • Sanatan Najeriya ya mika sakon ta'aziyya ga ahali da dangin wannan baiwar Allah da ta rasa ranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Gashua, jihar Yobe - Allah ya yiwa wata dalibar jami'ar tarayya da ke Gashua (FUGA) mai suna Shamsiyya Murtala rasuwa bayan tashin gobara a dakin kwanan dalibai a jami'ar.

Wannan mummunan lamarin ya auku ne a ranar Asabar 23 ga watan Maris na wannan shekarar, kamar yadda rrahoto ya bayyana.

Kara karanta wannan

Hotunan dan hazikin dan Najeriyan da ya kammala digiri da maki mai ban mamaki, ya sha kyautar kudi

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, wutar ta kama ne a dakin kwanan dalibai a lokacin da dalibar ke barci mai nauyi.

Allah ya yiwa daliba rasuwa bayan tashin gobara a jami'ar Yobe
Daliba ta mutu a gobara a jihar Yobe | Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi kokarin ceto Shamsiyya

An ruwaito cewa, sauran dalibai sun yi kokarin ceto ta daga wutar, amma suka gaza fasa kofar dakin don samun damar shiga.

Asibitin kwararru na Gashua ne ya tabbatar da mutuwarta bayan da aka tattara ta zuwa asibitin bayan bude kofar.

Wutar dai an ce ta yi barna a bangarori daban-daban na dakin kwanan daliban mata, musamman kadarori masu amfani kuma masu daraja.

Yaushe kuma ta yaya wutar ta kama?

Majiya ta bayyana cewa, wutar ta kama ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Asabar 23 ga watan Maris a daidai lokacin da daliban ke kan harkokin karatunsu.

Rundunar kashe gobara ta jami'ar da ta jiha sun kawo dauki, inda suka yi nasarar kashe wutar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta bayyana: Jigon LP ya bayyana dalilin da yasa Peter Obi ya yi buda-baki da Musulmai

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya mika sakon ta'aziyya, inda ya bayyana jimaminsa ga aukuwar lamarin.

Kasuwa ta kama da wuta a Abuja

A wani labarin, shahararriyar kasuwar Wuse da ke tsakiyar Abuja, babban birnin tarayya, ta kone kurmus a yammacin ranar Talata.

Ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba amma lamarin ya kawo karshen harkokin kasuwancin yau a yankin kasuwar.

Channels TV ta ruwaito cewa barkewar gobarar ta haifar da rufe dukkanin hanyoyin da ke kai wa zuwa kasuwar yayin da aka ga mutane suna gudun kai dauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel