Gwamnatin Tarayya Ta Ba da Sabon Umarni Kan Tallafin N50,000, Ta Fadi Ka’idoji

Gwamnatin Tarayya Ta Ba da Sabon Umarni Kan Tallafin N50,000, Ta Fadi Ka’idoji

  • Yayin da ake dakon tallafin Gwamnatin Tarayya na N50,000, ma’aikatar masana’antu da harkokin kasuwanci ta fitar da sabuwar sanarwa
  • Ma’aikatar ta bukaci wadanda suka cika tallafin su fara duba wayoyinsu domin samun sako daga FGGRANTLOAN kan ci gaba da tsare-tsare
  • Wannan na zuwa ne bayan tallafin da Gwamnatin Tarayya ke shirin bayarwa na N50,000 ga kananan ‘yan kasuwa da masu sana’o’i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ma’aikatar masana’antu da harkokin kasuwanci ta bukaci wadanda suka cika tallafin Gwamnatin Tarayya da su fara duba sakwanni a wayoyinsu.

Ma’aikatar ta bayyana haka ne a jiya Lahadi 24 ga watan Maris inda ta ce za a tura sakon ne daga FGGRANTLOAN.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan hari a Yobe, sun hallaka soja

Sabon umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan tallafin N50,000 ga 'yan Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta tura sabon umarni ga masu cin gajiyar tallafin N50,000. Hoto: Bloomberg, Picture Alliance.
Asali: Getty Images

Tallafin N50000: Wani umarni gwamnatin ta bada?

Sanarwar ta tabbatar da cewa wasu za su rasa damar samun tallafin saboda rashin hada lambar wayarsu da kuma lambar NIN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar masana'antu, Doris Nkiruka ta wallafa haka a shafinta na X a jiya Lahadi 24 ga watan Maris.

“A kula, wadanda suka cika tallafin Gwamnatin Tarayya na FGGRANTLOAN su fara duba wayoyinsu saboda shigowar sakwanni.”
“Sakon zai bukaci hada lambar waya da kuma lambar NIN wanda hakan zai saka a samu saukin gudanar da aikin.”
“Dole sunanka ya kasance cikin lambar NIN, idan ba haka ba za a rasa damar samun shiga, muna godiya da hakuri.”

- Doris Nkiruka

Yadda tsarin tallafin N50,000 zai kasance

Wannan tallafi zai taimakawa mata da kuma matasa domin inganta harkokinsu na kasuwanci da kuma sana’o’i.

Shirin zai zaga dukkanin kananan hukumomi 774 inda kaso 70 zai taimakawa mata da kuma matasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutane suna tsaka da Sallar Asham a watan Ramadana a Katsina

Har ila yau, kaso 10 za a raba ga mutane masu bukata ta musamman yayin da kaso 15 za a raba su ga sauran ‘yan kasa.

‘Yan Najeriya za su samu tallafin N50,000

A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na ba da tallafin N50,000 ga ‘yan Najeriya.

Tsarin zai tallafawa kananan ‘yan kasuwa da kuma masu sana’o’i domin inganta harkokinsu da suke yi na yau da kullum.

Wannan tallafin ya zo a dai-dai lokacin da ake cikin mawuyacin hali a kasar na tsadar kayayyaki musamman kayan abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.