Tinubu Zai Gwangwaje Mutanen Najeriya da Tallafin N50,000, an Fadi Tsarin Cin Gajiyar

Tinubu Zai Gwangwaje Mutanen Najeriya da Tallafin N50,000, an Fadi Tsarin Cin Gajiyar

  • Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin ba da tallafin N50,000 ga ƙananan 'yan kasuwa da masu sana'o'i
  • Shirin zai tallafa wurin inganta harkokin kasuwanci musamman bangaren ICT da sana'o'i da kananan 'yan kasuwa
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan kasuwar magani kan wannan tallafin domin bunkasa kasuwancinsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabuwar sanarwa kan ba 'yan Najeriya tallafin N50,000.

Wannan tallafi na daga cikin tsarin shugaban kasa Tinubu na ba da tallafin rage radadi (PCGS) domin kawowa jama'a saukin rayuwa.

Yan Najeriya za su fita daga takaici bayan Tinubu ya amince da ba da tallafin N50,000 ga 'yan kasar
Tallafin zai shafi dukkan kananan hukumomi 774 da ke fadin Najeriya. Hoto: State House.
Asali: Facebook

Wadanda za su ci gajiyar shirin Tinubu

Za a bada tallafin ne ga kananan 'yan kasuwa da kuma masu sana'o'i a fadin kasar domin rage radadin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

An cafke babban lauya da zargin kin biyan 'yar gidan magajiya bayan sun gama lalata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da bankin kasuwanci ya fitar, ya tabbatar da bangarorin da za su ci moriyar tallafin na Gwamnatin Tarayya.

Bangarorin sun hada da na kasuwanci da masu sana'o'i da sufuri da kafofin sadarwa da kuma masu sana'ar abinci.

Har ila yau, sanarwar ta tabbatar da cewa za a ba da tallafin ne ga wadanda suka cancanta ba tare da tilasta biyan kudin ba.

Za a ba mata da matasa muhimmanci

Shirin zai ba mata da matasa kaso 70 yayin da masu bukata ta musamman za su tashi da kaso 10, cewar Premium Times.

A cikin kaso 20 da ya rage, dattawa za su samu kaso biyar yayin sauran kaso 15 za a watsa su ga sauran jama'a.

Aƙalla mutane miliyan daya ne za su ci gajiyar shirin daga kananan hukumomi 774 da kuma birnin Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu na fuskantar sabuwar matsala yayin da 'yan fansho ke shirin fita zanga-zanga tsirara

An zabi wadanda za su ci gajiyar ne ta amfani da lambobin NIN da kuma BVN domin tabbatar da harkokin kasuwancinsu.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan kasuwar magani kan wannan tallafi na Tinubu.

Dan kasuwar mai suna Abubakar Umar Usman ya ce wannan mataki ya yi dai-dai inda ya yi fatan tallafin isa inda ya kamata.

Ya ce:

"Mu na maraba da kuma farin ciki bisa wannan kyakkyawan yunkuri na Gwamnatin Tarayya.
"Fatan dai Allah ya sa tallafin ya isa hannun wadanda su ka dace a tallafawa."

Kwastam za ta raba abinci

Kun ji cewa Hukumar Kwastam za ta sake raba abinci bayan ta sake kwato kayan abinci makare a cikin tirela a bakin iyakar Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta dukufa wurin dakile fita da kayan abinci wajen kasar ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel