Kasashen Spain, Ireland, Malta, Slovenia Sun Amince Su Yi Aiki Wajen ’Yantar da Falasdinu

Kasashen Spain, Ireland, Malta, Slovenia Sun Amince Su Yi Aiki Wajen ’Yantar da Falasdinu

  • Kasashen Turai hudu sun bayyana goyon bayansu ga cin gashin Falasdinu a matsayin kasa mai 'yanci
  • Spain ce ta bayyana hakan bayan wata ganawa da aka yi tsakanin kasashen a Ireland a ranar Juma'ar da ta gabata
  • Rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu na ci gaba da sanadiyyar mutuwar mutane da dama, shekaru sama da 70

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Madrid, Spain - Kasar Spain ta amince da shugabannin Ireland, Malta da Slovenia, da su dauki matakin farko na amincewa da 'yancin Falasdinu.

Wannan na fitowa ne daga firayim minista Pedro Sanchez a ranar Juma'a bayan wani taron Majalisar Turai a Brussels.

Kara karanta wannan

Mun tada matattu sama da 50 a cocina bayan tabbatar da mutuwarsu, inji malamin coci Chris

Da yake magana a madadin Spain, Sanchez ya bayyana tsammanin amincewar 'yancin ta faru a tsawon lokacin majalisar dokoki ta shekaru hudu da ta fara a bara.

Spain da wasu kasashe na son Falasdinu ta samu 'yancin kai
Ana neman Falasdinu ta samu 'yancin kai | Hoto: Reddit, Arab News
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka zo da yarjejeniyar amincewar

Ya shaida wa manema labarai cewa an cimma yarjejeniyar ne bayan ganawa da takwarorinsa na kasashen Ireland da Malta da kuma Slovenia a gefen taron majalisar a safiyar Juma’a 22 ga watan Maris, Arab News ta ruwaito.

Wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar ta ce:

"Mun amince da cewa hanya daya tilo da za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, ita ce ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta kasashe biyu, tare da zaman kafada da kafada da juna, cikin lumana da tsaro."

Akwai kasashen da suka amince Falasdinu kasa ce?

Kasashen Larabawa da kungiyar Tarayyar Turai sun amince a wani taron da suka yi a kasar Spain a watan Nuwamba cewa, cin gashin kan Falasdinu a matsayin kasa mai 'yanci kamar Isra'ila ne mafita ga rikicin kasashen biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

Tun daga shekarar 1988, kasashe 139 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya suka amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta, rahoton Reuters.

Yadda bam ya kashe jama'a masu sahur a Gaza

A wani labarin, bayan sojojin Israila sun tarwatsa su, mutane daga dangin Tabatibi a Falasdin sun tare a tsakiyar Gaza, amma ba su tsira ba.

Rahoton da aka samu daga tashar Aljazeera ya tabbatar da cewa an kai wani hari ta sama da ya kashe wadannan mutane a Gaza.

A yayin da Bayin Allah suke shirin yin sahur a ranar Juma’a, sai aka yi masu luguden wutar da tayi sanadiyyar kashe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel