'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Suna Tsaka da Sallar Asham a Watan Ramadana a Katsina
- An bayyana yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka kai farmaki tare da kashe mutane biyu a Katsina
- An sace wasu adadi a jihar, inda jami'an tsaro suka yi nasarar ceto su nan take bayan aukuwar lamarin
- Farmakin 'yan bindiga a Arewacin Najeriya na ci gaba da daukar bakin salo na mugunta a 'yan kwanakin nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Faskari, jihar Katsina - Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun hallaka mutane biyu suna tsaka Sallah a kauyen Mairuwa da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, Abubakar Aliyu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Punch ta wayar tarho a ranar Lahadi.
A cewar Sadiq, binciken farko ya nuna cewa, ‘yan bindigar da suka kai farmaki kauyen sun kashe mutum biyu sannan suka yi awon gaba da wasu mazauna kauyen a lokacin da suke tsaka da Sallah a Ramadana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ceto wadanda aka sace
Daga baya ‘yan sanda tare da wasu jami’an tsaro sun yi nasarar ceto wadanda aka sacen.
Sadiq ya kara da cewa, rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma ana kokarin cafke wadanda suka aikata wannan bakin aika-aika.
Jihar Katsina na daga jihohin Arewa masu Yammacin Najeriya da ke yawan fuskantar sace-sace da fashin 'yan bindiga.
Yadda lamarin ya faru
Shugaban karamar hukumar Faskari Musa Ado Faskari ya tabbatar da kashe mutanen biyu, inda yace tabbas an kashe su na sadda suke Sallar Tarawih, rahoton Vanguard.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Faskari ya ce an kai harin ne a lokacin Sallar Tarawihi ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki ne gidan Alhaji Lado Mairua a lokacin da ake Sallah, inda suka bukaci ya bi su amma ya ki. Don haka, suka harbe shi har lahira.
Limami ya mutu yana tsaka da sallah
A wani labarin kuma, al’amari mai taba zuciya ya auku a kasar Indonesia, inda wani limami ya rasu yana tsaka da sallah tare da mamu a wani masallaci.
A bidiyon da Legit Hausa ta samo, an ga lokacin da limamin ya tada raka’a, har ta kai ga ya yi sujjuda, sujjadar karshe kenan a rayuwarsa.
A cewar Abdulfatah Ayofe, wani ma’abocin Twitter da ya yada bidiyon a shafinsa, lamarin ya auku ne a ranar 2 ga watan Janairun wannan shekarar da muka shiga.
Asali: Legit.ng