Karyar Annabta: Karyar wani fasto dake tayar da matattu ta kare
Karyar wani Fasto dake ikirarin annabta tare da tayar da matattu a kasar Habasha ta kare bayan da ya kasa tayar da gawar wani mutum da ya mutu, kwanaki hudu da suka gabata.
Jami’an ‘yan sanda sun kama Faston, Getayawkal Ayele, bayan kasa tayar da gawar mutumin da ya mutu a wani garin yammacin kasar Habasaha da ake kira Galilee a jihar Wollegga.
A wani faifan bidiyo da yake yawo a dandalin sada zumunta a yanar gizo, an ga Faston, yayin da jami’an ‘yan sanda suka ritsa shi, a kan akwatin mamacin yana kiran sunansa da niyyar zai tayar da shi.
DUBA WANNAN: Ku rage yawan haihuwa domin 'ya'yanku su samu ilimi - Ganduje
Fasto Ayele ne tunda farko ya samu dangin mamacin tare da shaida masu cewar zai tayar dashi bayan ya kafa masu hujja da yadda Yesu Almasihu ya tayar da matacce kamar yadda BBC ta wallafa.
Bayan dangin mamacin da ake kira Belay Biftu sun amince ne sai aka nufi inda aka binne shi domin bawa Faston dammar tayar da shi.
Fasto Ayele ya saka jama’a sun tone kabarin sannan ya bude likkafanin da aka rufe gawar tare da yin ihu yana cewa “Beley ka tashi, Beley ka dawo”. Haka ya dauki lokaci mai tsawo yana safa da marwa a kan kabarin har saida jama’ar da suka taru suka gaji da kallon abinda yake yi ba tare da wani abu ya faru ba.
Hukumar ‘yan sanda ta kama Fasto Ayele bisa tuhumarsa da laifin cin mutuncin gawa, laifin dake sahun manyan laifuka a kasar Habasha.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng