'Yan sanda sun kama wani mai iƙirarin 'Annabta' da ya ce zai tayar da matattu

'Yan sanda sun kama wani mai iƙirarin 'Annabta' da ya ce zai tayar da matattu

- Rundunar yan sanda ta cafke mutum da ke kiran kansa Annabi Onyebuchi Okocha kan ikirarin cewa zai tada matattu

- Rundunar ta ce abinda ya ke aikatawa laifi ne kuma ta gargadi asibitoci da wuraren ajiye gawarwaki kada su sake suyi maraba da shi

- A kwanakin baya Okocha ya fitar da wani faifan bidiyo inda ya nuna gardawa ba tare da tufafi a jikinsu ba a cikin rafi yana watsa musu kudade

Rundunar yan sanda a jihar Anambra ta kama wani fasto da ke kiran kansa Annabi Onyebuchi Okocha da aka fi sani da 'Onyeze Jesus' kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Onyeze Jesus a cikin wani sakon da ya wallafa a faifan bidiyo ya yi ikirarin cewa zai tada gawarwakin mutane bakwai da ke ajiye a dakin ajiye gawarwarki na asbiti wato 'mortuary'.

'Yan sanda sun kama wani mai iƙirarin 'Annabta' da ya ce zai tayar da matattu
'Yan sanda sun kama wani mai iƙirarin 'Annabta' da ya ce zai tayar da matattu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Fitaccen mai wa'azin shine wanda ya kafa cocin Children of Light Anointing Ministries, Nkpor, a karamar hukumar Idemili North a jihar.

An kama shi ne a ranar Laraba 27 ga watan Janairun shekarar 2021.

Gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan watsa labarai da wayar da kan al'umma na jihar, MR C. Don Adinuba, a ranar Juma'a, 25 ga watan Janarun 2021 ta gargade shi kan ayyukan da ya ke yi da gwamnatin ta ce 'laifi ne da rashin tarbiyya da sunan addini.

Kazalika, Ma'aikatan Lafiya na Jihar, a sanarwar da ta fitar a ranar Laraba ta gargadi asibitoci a jihar da masu ajiye gawarwaki kada su sake su bari mutumin ya shiga wurin da suke ajiye gawarwaki da sunan zai tada matattu da siddabaru.

KU KARANTA: Wasu daga cikin yan matan Chibok sun sake tsere wa daga hannun yan Boko Haram

Mutane da dama sun bayyana damuwarsu a kafafen sada zumunta kan bidiyon da Onyeze Jesus ya fitar na gardawa ba tare da kaya a jikinsu ba a cikin rafi yana watsa musu kudade da sunan wai za su yi arziki.

Kakakin yan sandan jihar, CSP Haruna Mohammed ya tabbatar da kama shi inda ya ce nan bada dadewa ba za a gurfanar da shi a kotu.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel