Rashin Tsaro: Atiku Ya Caccaki Shugaba Tinubu, Ya Fadi Hanyar Kawo Karshen Matsalar

Rashin Tsaro: Atiku Ya Caccaki Shugaba Tinubu, Ya Fadi Hanyar Kawo Karshen Matsalar

  • Atiku Abubakar ya koka kan yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da ta'azzara a faɗin ƙasar nan ba dare ba rana
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyyana cewa Najeriya yanzu ta koma filin mutuwa a ƙarƙashin mulkin Bola Tinubu
  • Ya yi kira da a gaggauta yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ta yadda za a samar da ƴan sandan jihohi domin kawo ƙarshen matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da harin ta'addancin da aka kai a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.

An dai kai harin ne a ƙauyen Madaka wanda ya yi sanadiyyar rasuwar Magajin Garin da wasu mutum 20.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Daga karshe an fadi dalilin da ya sa aka kashe jami'an tsaron

Atiku ya caccaki Tinubu
Atiku ya caccaki Tinubu kan matsalar rashin tsaro Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Harin ya auku ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari a kasuwar ƙauyen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Atiku ya ce kan harin?

Da yake mayar da martani game harin, Atiku a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Juma'a, ya ce Najeriya ta zama "filin mutuwa" a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.

Ya yi kira da a gaggauta samar da ƴan sandan jihohi.

A kalamansa:

“Abin takaici ne yadda Najeriya ta zama filin kisa. Kashe mutane da dama da suka haɗa da Magajin Gari, a ranar Alhamis da kuma sace wasu da ba a tantance adadinsu ba da wasu ƴan bindiga suka yi a ƙauyen Madaka da ke ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja, wani tabbaci ne cewa saɓanin tabbacin da ake bayarwa, matsalar rashin tsaro na ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar mu.

Kara karanta wannan

Daukar nauyin ta'addanci: Sheikh Gumi ya fadi abin da ya dace a yi wa Tukur Mamu

"Dole ne mu ba da fifiko kan tsaro tare da hanzarta aiwatar da gyaran kundin tsarin mulki wanda zai samar ƴan sandan jihohi ta yadda jihohi da ƙananan hukumomi za su iya fito da hanyoyin da suka dace da yankinsu wajen magance wannan matsalar rashin tsaro a ƙasar mu.
"Ina alhini da addu’a ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma gwamnati da al’ummar jihar Neja.”

Batun ficewar Atiku jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya yi martani kan jita-jitar cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana rahoton a matsayin zuƙi ta malle wanda wasu ƴan baranda ke yaɗawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng