Obasanjo Ya Kebe Sabon Gwamna, Ya Shawarci Sauran Gwamnoni Suyi Koyi da Shi

Obasanjo Ya Kebe Sabon Gwamna, Ya Shawarci Sauran Gwamnoni Suyi Koyi da Shi

  • Olusegun Obasanjo ya bada misali da Alex Otti ganin yadda gwamnatinsa ta shafe fanshon tsofaffin gwamnonin Abia
  • Ana ware miliyoyin kudi ana biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu, gwamnatin Abia ta soke wannan tsari
  • Obasanjo ya ce gwamna Otti ya kyauta da ya kawo karshen abin da ya kira fashi da ake yi wa dukiyar talakawa a jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abia - Olusegun Obasanjo ya yabawa Mai girma Gwamna Alex Otti saboda yunkurin da ya kawo na rage kashe dukiyar al’ummarsa.

Cif Olusegun Obasanjo ya jinjinawa Gwamna Alex Otti ne a sakamakon soke wata dokar fansho da gwamnatinsa tayi a jihar Abia.

Obasanjo
Olusegun Obasanjo ya yabi Gwamna Alex Otti saboda soke fanshon gwamnoni a Abia Hoto: @Nedunaija
Asali: Twitter

Tsohon shugaba Obasanjo ya yabi Alex Otti

Gwamnoni da mataimakansu su kan karbi makudan kudi da sunan fansho, The Cable ta ce Obasanjo ya ji dadin yin watsi da ita.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malam Nasiru El-Rufa'i ya gana da fitaccen sanatan PDP, hotuna sun bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban na Najeriya ya yi kira ga sauran gwamnonin jihohi suyi koyi da Alex Otti a wajen rage yin facaka da baitul-mali.

Obasanjo ya ziyarci Gwamna Otti a Abia

Obasanjo ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan a Nvosi a karamar hukumar kudancin Isialangwa.

A yayin da yake garin gwamnan a jihar Abia, Obasanjo ya taya Otti murnar awo karshen kudin da ake biyan tsofaffin gwamnoni.

Obasanjo: "Fashin tsofaffin gwamnoni a Najeriya"

Rahotonni sun ce tsohon shugaban kasar ya bayyana fanshon tsofaffin gwamnoni da mataimakansu a matsayin fashi da rana tsaka.

"Fanshon tsofaffin gwamnoni tamkar fashi da rana tsaka ne domin yana ba su damar mallakar gida a Abuja da wani wurin"
"Sannan suyi gaba da duk abin da suka ga dama amma ba a biyan sauran al’umma fanshonsu, wani irin shugabanci kenan?"

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya sake cin karo da babbar matsala kan takarar da yake nema karo na 2

"Sai ka zo kuma ka ce dole a kawo karshen rashin gaskiyar. Ina taya ka murna, kuma dole in yi fatan abokan aikinka suyi koyi."
"Ka fara amma ka da ka taba gajiya. Wasu za su kashe maka kwarin guiwa, za a kira ka da sunaye."

- Olusegun Obasanjo

A rahoton tashar Channels, Obasanjo ya ce da za a samu irin Alex Otti da an cigaba, yake cewa gwamnan ya kawo cigaba a mulkin Abia.

Yadda za a farfado da Naira a Najeriya

Kwanaki an ji Ahmed Adamu wanda malami ne a jami’ar Nile da ke Abuja ya fadawa CBN matakan da za a bi domin Naira ta tashi.

Dr. Ahmed Adamu wanda ya kware a bangaren ilmin tattalin arziki ya nuna idan aka biyewa dabararsa, $1 za ta iya komawa N160.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng