Rashin Lafiya: Kotu Ta Ɗauki Mataki Kan Wanda Ake Zargi da Kashe Basarake a Arewa
- Wata kotun majistare a jihar Kwara ta dauki mataki kan Olowofela Oyebanji, wanda ake zargi da kashe Sarkin Kwara, Oba Peter Aremu
- Mai shari'a Monisola Kamson ya bayar da belin wanda ake zargin bayan da lauyansa ya karbo umarnin belin daga babbar kotun jihar.
- Barista Udeh, ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa ba zai iya gurfanar gaban kotun a yanzu na saboda tsananin rashin lafiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kwara - Babbar kotun jihar Kwara ta ba da belin daya daga cikin wadanda ake zargi da kashe Sarkin Kwara, Oba Peter Aremu, bisa rashin lafiya.
Wanda ake zargin, Olowofela Oyebanji, shi ne wanda ake tuhuma na biyu a cikin wadanda aka gurfanar a gaban Mai shari'a Monisola Kamson bisa zargin aikata laifin kisan kai.
Dalilin ba da belin Oyebanji
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Lauyan Oyebanji, Barista Udeh, ya bayyanawa kotun majistare cewa ya karbo umarnin bayar da belin wanda yake karewa daga babbar kotun jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a halin yanzu Oyebanji ba zai iya gurfanar da kansa a gaban kotu ba saboda yana kwance a wani asibitin jihar Legas.
Sai dai ya yi alkawarin tabbatar da gurfanar da shi a ranar da za ayi zaman kotun na gaba.
Mutane 13 ake zargi da kashe Aremu
Mai shari'a Kamson, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 9 ga Afrilu, 2024.
Wannan na zuwa ne bayan da kotun a kwanakin baya ta bayar da umarnin garkame mutane 13 a gidan yari bisa zargin kishe basaraken, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.
An yi zargin cewa sun kashe Aremu ne a fadarsa a yayin da ya ke shirin cin abincin dare bayan dawowa daga wani taro na tsaro.
An yi zanga-zaga a fadar Sarkin Ilorin?
A baya-bayan nan, rahotanni suka riƙa yawo na cewa maza da mata sun gudanar da zanga-zanga a fadar Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari.
Sai dai wani rahoto na Legit Hausa ya nuna cewa labaran ƙarya ne ake yaɗawa kamar yadda fadar sarkin ta tabbatar.
Sarki Sulu-Gambari ya ce faifan bidiyo da ke nuna cewa jama'a sun yi wa fadarsa tsinke suna kukan yunwa ba gaskiya ba ne, kirkira ce ta magauta.
Asali: Legit.ng