Tsadar Rayuwa: Zanga-Zanga Ta Barke a Fadar Babban Basarake a Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Tsadar Rayuwa: Zanga-Zanga Ta Barke a Fadar Babban Basarake a Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Sarkin Ilorin a jihar Kwara ya ce wani faifan bidiyo da ke nuna "mummunar zanga-zanga" a fadarsa na ƙarya na
  • Sarkin ya ce game da wahalhalun da Najeriya ke ciki a yanzu, sarakunan gargajiya a jihar Kwara suna tattaunawa da gwamnati a kowane mataki
  • Sarkin ya bayyana cewa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq mutum ne mai fahimta kuma ya damu da talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ilorin, jihar Kwara - Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, a ranar Lahadi, 18 ga watan Fabrairu, ya yi martani kan wani faifan bidiyo da ke nuna ana zanga-zanga a fadarsa.

Sarkin ya bayyana wani faifan bidiyon wanda wasu mutane ke kururuwa da koke-koke kan talauci da wahalhalun da ake fuskanta a Najeriya a ƙofar fadarsa a matsayin na ƙarya ne.

Kara karanta wannan

Kamfanin BUA zai yi wa ma'aikatansa abu 1 bayan ya kara farashin buhun siminti

Sarkin Ilorin ya karyata bidiyon zanga-zanga
Sarkin Ilorin ya musanta bidiyon yin zanga-zanga a fadarsa kan tsadar rayuwa Hoto: @RealAARahman
Asali: Twitter

Sarkin ya bayyana cewa faifan bidiyon ba ya da alaƙa da halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu domin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara shugaba ne mai jin ra’ayin jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me basaraken ya ce kan bidiyon zanga-zangar?

Martanin basaraken na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunsa Abdulazeez Arowona.

Sarkin ya buƙaci jama’a da su yi watsi da faifan bidiyon da ake yadawa “domin kauce wa yin kuskuren fahimtar abin da ba shi ba ne a cikin bidiyon".

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Bidiyon ba shi da wata alaƙa da halin da ƙasar nan ke ciki, kuma za a iya tunawa a lokuta irin haka, Sarkin Ilorin kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Kwara, Alhaji (Dr) Ibrahim Sulu-Gambari CFR, ya kan bayyana ra’ayinsa kan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ayyana yin azumin kwana 1 a Borno, ya fadi dalili

"Dangane da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ake fama da shi, Sarkin da takwarorinsa a matakin majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kwara suna jan hankalin gwamnati a kowane mataki kan buƙatar ci gaba da inganta walwala, tsaro da zamantakewar al’ummar jihar tare da yaba wa gwamnatin jiha saboda yadda take mai da martani ga al'amuran da suka shafi talakawa.
"Don haka muna kira ga jama'a da su yi watsi da faifan bidiyon da ke yawo don gujewa yin kuskure kan abinda bidiyon ya ƙunsa da wurin da aka ɗauke shi."

Jigon PDP Ya Faɗi Laifin 'Yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban jigo a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya bayyana kuskuren da ƴan Najeriya suka yi kan halin da ake ciki a ƙasar nan

Tsohon ɗan takarar gwamnan na jihar Ogun ya bayyana cewa ƴan Najeriya suna sane da irin wahalar da suka sha a gwamnatin APC, amma suka sake zaɓenta ta ci gaba da mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel