Tinubu Ya Aike da Muhimman Buƙatu 2 Ga Majalisa Kan Kasafin Kuɗin da Ya Gada Daga Buhari

Tinubu Ya Aike da Muhimman Buƙatu 2 Ga Majalisa Kan Kasafin Kuɗin da Ya Gada Daga Buhari

  • Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar wakilai ta ƙasa ta kara masa wa'adin aiwatar da tanadin dokar kasafin kuɗin 2023
  • Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas ne ya bayyana haka yayin da yake karanta wasiƙar Tinubu, ya kuma nemi tsawaita wa'adin karin kasafin
  • Shugaban ƙasar ya ce wannan bukata ta zama dole domin ta haka ne zai samu damar kammala dukkan ayyukan da ke cikin kasafin guda biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da saƙo ga majalisar wakilan tarayya kan kasafin kuɗin 2023 da ya gada daga Muhammadu Buhari.

Tinubu ya buƙaci majalisar ta tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin kuɗin daga ranar 31 ga watan Maris, 2024 zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2024, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun samu ƙarin kuɗin shiga a 2023 saboda abu 1

Shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya nemi tsawaita wa'adin kasafin kuɗin 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

Wannan buƙata na ƙunshe a wata wasiƙa da Bola Tinubu ya tura kuma shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta a zauren majalisar ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, shugaban kasar ya bukaci majalisar ta tsawaita lokacin aiwatar da dokar ƙarin kasafin kuɗin 2023, shi ma daga 31 ga watan Maris zuwa 30 ga watan Yuni, 2024.

Bola Tinubu ya ce tsawaita wa’adin ya zama dole domin tabbatar da cewa an aiwatar da ayyukan da ke kunshe a dokokin kasafin guda biyu gaba daya.

Majalisa ta amince da buƙata 1

Jaridar Punch ta tattaro cewa majalisar wakilan ta amince da tsawaita wa'adin aiwatar da dokar ƙarin kasafin kuɗin 2023 kamar yadda shugaban kasa ya nema.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kace-nace kan zargin cushe a kasafin kuɗin 2024 waɓda ya fara fitowa daga bakin sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Shugaba Tinubu ya fadi lokacin da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

An nemi Akpabio ya yi murabus

A wani rahoton na daban kun ji cewa gamayyar ƙungiyoyin fararen hula a Bauchi sun yi tir da matakin majalisar dattawa na dakatar da Sanata Abdul Ningi.

Sun yi kira ga Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus domin ba da damar bincike kan zargin cushen kuɗi a kasafin kuɗin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel