Nyako: An Gano Yadda Buhari Ya Yi Kokarin Amfani da Minista a Shari’ar Tsohon Gwamna
- Yayin da ake ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan Adamawa, Murtala Nyako, an gano yadda Muhammadu Buhari ya yi kokarin taimakonsa
- Tsohon Atoni-janar, Michael Aondoakaa ya ce Buhari ya yi iya bakin kokarinsa domin ganin an janye karar da ake yi kan Nyako
- Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Nyako wanda ya mulki jihar daga shekarar 2011 zuwa 2015 kan badakalar N29bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Tsohon Ministan Shari’a, Michael Aondoakaa ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya so yin afuwa ga tsohon gwamnan Adamawa, Murtala Nyako.
Aondoakaa ya ce Buhari ya yi kokarin kawo karshen shari’ar da ake yi kan Nyako saboda shekarunsa.
A kan me ake zargin Nyako, dansa?
Ana zargin Nyako mai shekaru 81 wanda ya mulki jihar daga shekarar 2008 zuwa 2014 da kuma dansa Abdul’aziz Nyako kan badakalar N29bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sake gurfanar da Nyako ne da dansa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja a yau Alhamis 21 ga watan Maris, cewar Premium Times.
Jim kadan bayan gurfanar da tsohon gwamnan, Aondoakaa wanda tsohon lauyan gwamnan ne ya ce Buhari ya umarci tsohon Atoni-janar, Abubakar Malami domin a janye tuhume-tuhumen.
Ya ce Buhari ya nemi Malami da ya samu hukumar EFCC domin ganin an janye karar Nyako da ake yi.
“Sai dai siyasa ta lalata komai saboda Malami a lokacin yana kokarin zama gwamnan jihar Kebbi.”
- Michael Aondoakaa
Nyako: Matakin da alkalin kotu ya dauka
Wannan martani na Aondoakaa ya sa lauyan masu kara, Oluwaleke Atolagbe ya fadawa kotun cewa Nyako ya so yarjejeniya da gwamnati domin ta masa afuwa.
Bayan wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan, alkalin kotun ya bukaci ba shi beli kan dokokin da aka bayar a baya, cewar Vanguard.
Daga bisani, alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar 10 ga watan Mayun wannan shekara.
Emefiele ya cire daloli babu sanin Buhari
Kun ji cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya cire makudan kudi na daloli a mulkin Buhar ba tare da ya sani ba.
Hadimin Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka inda ya ce mafi yawan abubuwa da suka faru a wancan lokaci Buhari bai sani ba.
Asali: Legit.ng