Kisan Sojoji 16: Majalisar Dattawa Tana Ganawar Sirri da Hafsoshin Tsaro, an Samu Bayanai

Kisan Sojoji 16: Majalisar Dattawa Tana Ganawar Sirri da Hafsoshin Tsaro, an Samu Bayanai

  • Yayin da ake ci gaba da bincike kan kisan sojoji a jihar Delta, Majalisar Dattawa ta shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro
  • Majalisar ta sanar da cewa za ta yi ganawar ne domin binciken makasudin ta'asar da aka yi kan sojoji 16 a cikin sirri
  • Wannan ya biyo bayan kisan sojojin da aka yi a kauyen Okuama da ke jihar Delta yayin da suka je kwantar da tarzoma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanatoci da hafsoshin tsaro a Najeriya sun shiga ganawar sirri kan kisan sojoji 16 a jihar Delta.

Hafsoshin tsaron sun gurfanar ne a gaban kwamitocin sojojin ruwa da na sama da kuma na kasa kan fara bincike game da lamarin a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Yadda rikicin gona ya yi sanadin kashe sojoji 17 a jihar Delta, in ji shugaban al'umma

Majalisa ta titsiye hafsoshin tsaro kan kisan sojoji a jihar Delta
Majalisa ta na ganawar sirri da hafsoshin tsaro kan kisan sojoji a jihar Delta. Hoto: Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Hafsoshin sojoji da suka gana da Sanatoci

Shugaban kwamitin, Sanata Ahmed kasan ya ce za suyi ganawar binciken kisan sojojin ne a cikin sirri, a cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga wadanda suke cikin ganawar akwai Hafsan sojojin ƙasa, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja da takwaransa na sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar.

Sauran sun hada da hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla da kuma hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa, cewar The Nation.

Sojoji: Umarnin da Majalisar ta bayar a baya

Wannan ganawar sirrin na zuwa ne bayan kisan sojoji 16 a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Majalisar a ranar Talata 19 fa watan Maris ta umarci dukkan jami'an tsaron da su hada kai rundunar sojojin ƙasa domin yin bincike.

Rundunar tsaron a ranar Litinin 18 ga watan Maris ta fitar da hotunan sojojin da aka hallaka yayin da suka kai dauki domin kwantar da tarzoma a yankin.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 16: Majalisar dattawa ta dauki muhimmin mataki

Wasu fusatatttun sojoji sun kona kauyen Delta

Kun ji cewa ana zargin wasu fusatattun sojoji sun bankawa kauyen Okuoma wuta a jihar Delta kan kisan jammi'ansu.

Sojojin sun dauki matakin ne bayan wasu bata gari sun yi ajalin sojoji 16 a kauyen da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

Wannan mataki na sojojin ya jawo kace-nace inda wasu ke ganin daukar matakin bai dace ba a wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel