Cikakken Jerin Sunayen Mutum 9 da Ƴan Canji 6 da ke Ɗaukar Nauyin Ta'addanci Ciki Har da Abokin Gumi
- Gwamnatin tarayya ta ayyana Tukur Mamu, ɗan jarida a Kaduna da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya
- Tun a watan Satumba na shekarar 2022, hukumar tsaron farin kaya (DSS) ke tsare da Mamu, wanda ke fuskantar shari'a kan zargin alaƙa da ƴan ta'adda
- Daga cikin waɗanda gwamnati take zargin suna taimakawa ta'addanci, akwai ɗaiɗaikun mutane 9 da kuma ƴan canji da kamfanoni 6
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Kwamitin NSC mai sanya takunkumi ya yi biyayya ga umarnin gwamnatin tarayya wajen bayyana sunayen waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Waɗanda ake zargin sun kunshi ɗaiɗaikun mutane tara da kuma ƴan canji da kamfanoni shida.
Dukkansu dai suna cikin takunkumi saboda zargin da ake masu da hannu a ayyukan ta'addanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sunayen mutanen da ake zargi
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, sunayen mutanen da ake zargin sune;
1. Tukur Mamu
2. Yusuf Ghazai
3. Muhammad Sani
4. Abubakar Muhammad
5. Sallamuddeen Hassan
6. Adamu Ishak
7. Hassana Oyiza Isah
8. Abdulƙareem Musa
9. Umar Abdullahi
Ƴan canji da wasu kamfanoni
10. Kamfanin West and East Africa General Trading
11. Kamfanin canjin kuɗi na Settings Bureau De Change Limited
12. Kamfanin G. Side General Enterprises
13. Desert Exchange Ventures Limited
14. Kamfanin Eagle Square General Trading
15. Na ƙarshe shi ne kamfanin canji na Alfa Exchange BDC
A ranar Talata da ta gabata, hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya ta bayyana wannan ci gaban.
Sanarwar ta ce kwamitin sanya takunkumi na kasa (NSC) ya zauna ranar 18 ga watan Maris, 2024, inda aka tattauna kan waɗannan mutane da kamfanonin.
A taron, kwamitin ya duba batun sanya masu takunkumi saboda zarginsu da hannu wajen angiza wa ƴan ta'adda kuɗaɗe.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka ga sunansu a farko-farko, Tukur Mamu, ɗan jarida mazaunin Kaduna, yana fuskantar shari'a kan zargin taimakawa ƴan ta'addan da suka faramki jirgin ƙasan Kaduna-Abuja.
Kamar yadda yake ƙunshe a takardar, ana tuhumar Mamu da hannu a turawa ƴan ta'addan ISWAP kudi da suka kai $200,000 domin sako fasinjojin jirgin, Channels tv ta ruwaito.
An kama wanda ya yi barazanar kashe shugaban EFCC
A wani rahoton kuma Dakarun EFCC sun cafke mutumin da ya yi barazanar kashe shugaban hukumar, Ola Olukoyede bayan ya bankaɗo sirrin watan ƙungiyar addini.
A watan Janairu, 2024, shugaban EFCC ya bayyana cewa sun gano wata ƙungiyar addini da ke safarar makudan kuɗi ga ƴan ta'adda a Najeriya.
Asali: Legit.ng