An Damke Tukur Mamu A Kasar Misra Bisa Umurnin Gwamnatin Tarayya

An Damke Tukur Mamu A Kasar Misra Bisa Umurnin Gwamnatin Tarayya

  • An damke mutumin da ke sulhun ceton fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna daga wajen yan bindiga
  • Rahoto ya nuna cewa jami'an tsaro sun damke Tukur Mamu a Kahira, babbar birnin kasar Masar
  • Tukur Mamu tare da iyalansa sun bar Najeriya ranar Talata don zuwa Saudiyya yin Umrah

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jami'an tsaron birnin Kahira a kasar Masar sun damke mai kokarin sulhu tsakanin yan bindiga da iyalan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna tare da iyalansa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Tukur Mamu na hanyarsa ta tafiya kasar Saudiyya gudanar da Ibadar Umrah yayinda aka tsareshi a tashar jirgin Kahira na kwana guda.

Rahoton yan kara da cewa gwamnatin tarayya ce ta bukaci a damkeshi.

Tuku Mamu
An Damke Tukur Mamu A Kasar Misra Bisa Umurnin Gwamnatin Tarayya Hoto: Tukur Mamu
Asali: UGC

A hirar da akayi da shi, ya bayyana cewa bayan gudanar da bincike kansa da jami'an tsaron Masar sukayi, basu sameshi da wani aibi ba.

Kara karanta wannan

Rivers: N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mamu yace gwamnatin tarayya ta yi niyyar tsareshi kamar yadda aka yiwa mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho, amma hakan bai yiwu ba saboda gwamnatin Masar ta tarar dukkan takardunsa sahihai ne.

Rahoton ya kara da cewa yanzu haka ana hanyar dawo da shi Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel