Shugaba Tinubu Ya Nuna Damuwa Kan Abin da 'Yan Majalisu Ke Yi Wa Ministocinsa, Ya Kawo Mafita
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi buɗa baki tare da shugabannin majalisar wakilai a fadarsa da ke Villa
- Tinubu ya buƙaci ƴan majalisun da su rage yawan kiran ministocinsa da shugabannin hukumomi domin bayyana a gabansu
- Ya yi nuni da cewa yawan gayyato su zai iya kawo cikas wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roki ƴan majalisar wakilai da su rage kiran ministoci da shugabannin hukumomi domin bayyana a gaban kwamitocin majalisar.
Shugaba Tinubu ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗa baki tare da kakakin majalisar, Tajudeen Abbas da sauran shugabannin majalisar.
An dai shirya buɗa bakin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Maris, a faɗar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane ƙorafi Tinubu ya yi?
Tinubu ya ce yayin da sanya ido kan ayyukansu yana da muhimmanci domin tabbatar da gaskiya, yawan kiransu ka iya kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A bisa hakan, sai ya buƙaci ƴan majalisun da su riƙa kula sosai wajen gudanar da sa ido kan ayyukansu.
A kalamansa:
"Na daɗe ina ganin kwamitoci da dama suna gayyato ministoci da shugabannin hukumomi.
"Na yi wa kakakin majalisa ƙorafi a bar mutanen nan su sarara. A bar mutanen nan su yi aikinsu.
"Ba cewa mu kayi ba ku da ikon yin hakan ba ne. Ba cewa mu kayi ba za ku iya yin aikinku ba.
"Amma ku yi la'akari da aikin da ya rataya a wuyan kowace hukuma, ma'aikatanta, ko nauyin da ke kan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ko ministan kuɗi da tattalin arziƙi a gare ku da sauran al'umma baki ɗaya.
"Idan ana ɗauke musu hankali ko takura musu, ta yiwu sai mun riƙa ɗaga zaman majalisa har zuwa ƙarshen dare.
"Dole ne mu samu hanyar da za mu yi haƙuri da juna. Wannan roƙo ne a gare ku. Ku duba ku gani idan a wasu lokutan za ku iya yarda su turo wakilai ko takardu."
Tinubu ya tura saƙo ga majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da saƙo ga majalisar wakilan tarayya kan kasafin kuɗin 2023 da ya gada daga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Tinubu ya buƙaci majalisar da ta tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin kuɗin daga ranar 31 ga watan Maris, 2024 zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2024
Asali: Legit.ng