Wasu Ma’aikata Za Su Samu Karin Albashi, Tinubu Ya Aika Takarda Zuwa Ga Majalisar Tarayya
- Yayin da 'yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, Bola Tinubu ya bukaci yin gyaran fuska kan albashi da alawus na ma'aikatan shari'a
- Shugaban kasar ya tura bukatar ce domin tabbatar da inganta bangaren da kuma ganin ta tsaya da kafafunta ba tare da katsalandan ba
- Shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio shi ya karanto bukatar Tinubu yayin zamansu a yau Laraba 20 ga watan Maris
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta kawo kudirin da zai sake fasali kan albashi da alawus na ma'aikatan shari'a.
Bukatar na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanto, a cewar Tribune.
Karin albashi: Me takardar Tinubu ta kunsa?
Akpabio ya karanto bukatar ne yayin zaman majalisar a yau Laraba 20 ga watan Maris mai taken "Dokar albashin ma'aikatan shari'a da alawus ta 2024".
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu a cikin takardar ya ce sake fasalin albashin ma'aikatan zai kawo gyara a bangaren shari'a ta inganta ta, kamar yadda Premium Times ta tattaro.
Ya ce hakan zai taimaka wurin tabbatar da bangaren ta tsaya da kafafunta ba tare da katsalandan daga bangaren zartarwa ko Majalisa ba.
Muhimmancin kudirin karin albashin malaman shari'a
"Dokar sake fasalin albashi da alawus na ma'aikatan shari'a za ta kawo karshen tsawon lokaci da aka yi ba tare da samun karin kudi a bangaren ba."
"Dokar za ta inganta bangaren tare da tabbatar da ta tsaya kan kafafunta idan aka dabbaka ta."
"Ina fatan Majalisar za ta duba yiwuwar gyara fasalin albashi da kuma alawus na ma'aikatan shari'a."
- Bola Tinubu
APC ta gargadi Tinubu a Abuja
Kun ji cewa jam'iyyar APC a birnin Abuja ta tura sakon gargadi mai zafi ga Shugaba Bola Tinubu kan zaben 2027.
Shugabannin jamiyyar sun gargadi shugaban ne yayin da ya ke zargin ministan Abuja, Nyesom Wike ya na karfa-karfa a nadin mukamai.
Sun bukaci Tinubu ta taka masa birki ganin yadda ya ke kokarin cusa 'yan jami'yyarsa ta PDP madadin 'ya'yan jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng