Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Ceto Mutum 4 da Suka Sace
- Dakarun sojoji sun samu nasarar rage mugun iri na ƴan ta'addan da suke aikata ayyukan ta'addanci a ƙasar nan
- A yayin artabun da suka yi a jihohin Filato, Zamfara da Imo, jami'an tsaron sun sheƙe ƴan ta'adda biyu
- Sun kuma ceto wasu mutum huɗu da miyagun suka yi garkuwa da su bayan sun nuna musu ƙarfin damtse
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Dakarun sojojin Najeriya a jihohin Filato da Zamfara da Imo sun kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su.
Sojojin sun kuma kashe ƴan ta'adda guda biyu ciki har da ɗan ƙungiyar ƴan ta'addan IPOB/ESN, cewar rahoton jaridar Leadership.
A wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a X, ya ce sojojin da aka tura ƙaramar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Filato sun ceto wata Misis Rosemary Jekpe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ceto mutanen da aka sace
An ceto Rosemary ne a ƙauyen Rafinbuna da ke ƙaramar hukumar Bassa a jihar, bayan sun yi musayar wuta da masu garkuwa da mutane.
Ya ce an yi garkuwa da matar ne a gidanta da ke Abuja Layout, Bukuru Low Cost Housing a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Janar Nwachukwu ya ce sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da babura biyu daga hannun masu garkuwa da mutanen.
Jami'an sojoji sun shiga mafakar 'yan bindiga
Janar din ya ce sojojin sun kuma kai wani samame kan maɓoyar ƴan ta'adda a ƙauyen Zamtip da ke ƙaramar hukumar Wase a jihar Filato, bayan samun bayanan sirri.
A yayin farmakin sun cafke ɗaya daga cikin ƴan ta'addan, yayin da ɗayan saboda kada a cafke shi ya salwantar da kansa.
Dakarun Sojoji sun fatattaki ƴan ta'adda
A wani samame da aka kai a jihar Zamfara, sojojin bayan samun kiran gaggawa sun daƙile yunƙurin sace wasu mutum uku a ƙauyen Kwatarkwashi da ke ƙaramar hukumar Gusau.
Ya ce sojojin sun yi artabu tare da fatattakar ƴan bindigan, lamarin da ya tilasta musu barin mutanen uku waɗanda nan take sojojin suka ceto su.
Yadda Sojoji suka halaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa haziƙan Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan ta'adda huɗu a wani samame da suka kai a jihohin Kaduna da Katsina.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Asali: Legit.ng