Kaduna: "Sau 4 Tinubu Ke Kira Na Kullum", Uba Sani Ya Magantu Kan Matsalar Tsaro
- Yayin da ake fama da hare-haren 'yan bindiga a jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya yabawa Shugaba Tinubu
- Uba Sani ya ce shugaban Tinubu ya na cikin damuwa kan wannan matsala da jihar ke ciki na rashin tsari
- Ya ce a kullum Shugaban Tinubu ya na kiransa sau biyu zuwa huɗu domin sanin halin da suke ciki a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana yadda ya ke magana da Shugaba Tinubu kan matsalar tsaron jihar.
Uba Sani ya ce a kullum ya na magana da Tinubu akalla sau biyu domin ganin an shawo kan matsalar tsaron a jihar.
Himmatuwar Tinubu kan matsalar Kaduna
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa shugaba Tinubu da hafsoshin tsaro sun himmatu wurin tabbatar da kawo karshen matsalar tsaro a kasar.
"Tinubu ya na cikin damuwa kan wannan matsalar tsaro, ina magana da shi a kullum sau biyu, ya na nuna damuwa matuka kan lamarin."
"Ya himmatu kwarai da gaske, kuma na gamsu da abin da ya ke yi kan matsalar, na kuma gamsu da jami'an tsaronmu za a yi nasara a gaba."
"Mun yi zama da hafsoshin tsaro da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, sun damu matuka kan wannan matsalar."
- Uba Sani
Uba Sani ya yabawa Tinubu
Ya ce ya yi amanna da irin himmatuwar Tinubu wurin dakile a matsalar ganin yadda ya ke nuna damuwa cewar Daily Trust.
"Shugaban ya damu matuka, ya na kira na sau biyu, wata rana har sau hudu domin ya ji halin da jihar ke ciki na matsalar tsaro."
- Uba Sani
Gwamna ya kuma ce gwamnatinsa ta kawo wasu tsare-tsare game da tallafawa al'ummar jihar domin rage musu radadi.
Sojoji sun ceto mutane 16 a Kaduna
Kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kubutar da wasu mutane 16 daga hannun 'yan bindiga.
Sojojin sun samu wannan gagarumar nasara ce a kauyen Tantatu da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng