InnalilLahi: Yan bindiga Sun Yi Ajalin Babban Basarake a Bauchi Bayan Garkuwa da Shi
- Dagacin Riruwai da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi ya riga mu gidan gaskiya bayan 'yan bindiga sun yi ajalinsa
- Marigayin Alhaji Garba Badamasi ya rasa ransa ne bayan maharan sun kai hari kauyensa a ranar 15 ga watan Maris
- Daga bisani an tsinci gawarsa a daji inda aka dauke ta zuwa fadar dagacin Lame a Gumau tare da yi masa sallar jana'iza
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - 'Yan bindiga sun hallaka basaraken Riruwai a ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon lokaci.
Marigayin mai suna Alhaji Garba Badamasi ya hadu da tsautsayin ne a ranar 15 ga watan Maris bayan maharan sun kai hari a garin.
Yadda maharan suka kai hari kauyen Bauchi
Yan bindiga sun yi ta harbi tare da firgita mutanen yankin inda suka ci karensu babu babbaka a kauyen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin harin, maharan sun durfafi fadar Sarkin inda suka yi awun gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Mutanen kauyen sun shiga mummunan yanayi bayan bacewar basaraken cikin mawuyacin hali, cewar Newstral.
Daga bisani an tsinci gawarsa inda ya ke nuna alamun irin kisan gilla da maharan suka yi masa.
Martanin wani dagaci kan harin a Bauchi
Har ila yau, an dauki gawarsa zuwa fadar dagacin Lame a Gumau a ranar Lahadi 17 ga watan Maris inda aka yi sallar jana'izarsa.
Wani daga cikin dagatai a yankin ya tabbatarwa Tribune faruwar lamarin inda ya yi masa addu'ar samun rahama.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a Bauchi, SP Ahmed Wakili da wakilin Legit Hausa ya yi ya ci tura saboda ya ɗaga wayar ba tare da yin martani ba.
Daga bisani wakilin Legit Hausa ya sake tura sakon karta-kwana amma bai samu martani daga kakakin rundunar ba.
Sanatan Bauchi zai iya komawa kujerarsa
Kun ji cewa akwai alamun Sanata Abdul Ningi zai iya komawa kan kujerarsa bayan dakatar da shi a Majalisar Dattawa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana kan tattaunawa domin shawo kan matsalar cikin sauki ba tare da matsala ba.
Wannan na zuwa ne bayan dakatar da Ningi kan zargin da ya yi cewa an yi cushe a kasafin kudin shekarar 2024.
Asali: Legit.ng