A Madadin Yin Shagalin Biki, Budurwa Ta Ba da Mamaki, Ta Kashe Kudin Bikinta a Wani Abu Mai Amfani

A Madadin Yin Shagalin Biki, Budurwa Ta Ba da Mamaki, Ta Kashe Kudin Bikinta a Wani Abu Mai Amfani

  • Wata budurwar 'yar Najeriya ta sha yabo a kafar sada zumunta bayan da ta ba da mamaki a lokacin bikinta
  • Wannan na zuwa ne bayan da ta sanar da bude karamin kantin siyayya da kudin da ya kamata ta yi biki dasu
  • Ta bayyana abin da za ta yi kudin, wanda tuni ta nunawa duniya shagon da ta bude don nuna yanzu kam za ta shiga daga ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Wata mata 'yar Najeriya ta yada wani bidiyo mai daukar hankali a kafar sada zumunta na yadda ta shirya rayuwa mai kyau.

Ta bayyana bude kantin siyayya a madadin yin biki da kudin da suka ware domin yin biki a lokacin aurenta.

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

@yallallmeetkaphyblack ta taya kanta murnar bude wani kantin siyayya kana ta bayyana godiya ga mijinta da ya ba ta goyon baya.

Budurwar da ta ki biki, ta bude shago da kudin aurenta
A madadin ta yi biki, ta bude shago da kudin aurenta | Hoto: @yallallmeetkaphyblack
Asali: TikTok

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da yasa ta zabi shago

Ta yada bidiyo a TikTok tare da cewa:

"Eeeiii Nagode Allah ina kuma taya kaina Mammie Nelson murna bisa bude wannan kanti nagode mijina."

A bidiyon, matar ta nuna jin dadi tare da nunawa duniya abin da ta tara a cikin shagon nata da sunan fara kasuwanci.

Ta kuma bayyana cewa, kudin da ta bude shagon nan fa ba komai bane face kudin da suka tanada domin burge dangi a wajen bikinsu.

Ta kuma bayyana cewa, ta gwammac ta sanya zoben alkawarin aure a madadin sanya kayan kawa da kuma burge jama'a a lokacin bikinsu.

Kalli bidiyon shagon a kasa:

Martanin jama'a a kafar sada zumunta

Kara karanta wannan

Bayan rage farashin abinci, Gwamnan APC ya lissafo kasuwannin da za a iya samun kayan cikin sauki

Legit Hausa ta tattaro muku kadan daga cikin kalaman da mutane ke yi a kafar sada zumunta kan wannan lamari:

kindandgreat:

"Kai, nima fa abin da na yi kenan, haka ya bude min shagon kayan masarufi a haka muka gina gidanmu yanzu muna shirin aure."

idowuobiesie:

"Ina taya ki murna na yanke wannan shawari, ina ba ku shawarar yin aurenku a kotu da kuma dan karamin liyafa, me zai amfanar don an yi babban biki."

Adejoke Akewi toh standout:

"Ina taya ki murna 'yar uwa, abin da mijina ya fada min kenan a yi biki mai girma ko kuma ya bude min shago, nace shago nake so."

ronkeadekoya145:

"Nima fa haka ne 'yar uwa, haka mijina yace zai bude min shago a wancan lokacin bai da kudin kashewa a shirin biki kawai muka fara kasuwa."

Budurwa ta rabu da saurayin da ya bude mata shago

A wani labarin kuma, wata budurwa ta ci amanar saurayinta bayan da ya bude mata shago saboda ta taimaki kanta.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta kama Musulman da ke cin abinci a bainar jama'a ana azumi

Matashin shi ne ya taimaka mata ta bude shagon siyar da kayan sawa, amma daga baya sai budurwar ta rabu da shi.

A wani labari mai sosa zuciya da Wizarab ya sanya a shafinsa na X (wanda a baya aka sani da Twitter, matashin ya bayyana cewa yanzu arzikinsa ya dawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel