Matashi Ya Yi Wuff Da Kyakkyawar Budurwar Da Ya Kamu Da Sonta Lokacin Da Suka Fara Haduwa

Matashi Ya Yi Wuff Da Kyakkyawar Budurwar Da Ya Kamu Da Sonta Lokacin Da Suka Fara Haduwa

  • Wani kyakkyawan matashi ya yi wuff da wata budurwa bayan ya faɗa kogin sonta a lokacin farko da ya fara ganinta
  • Ƴar uwar matashin ta sanya labarin soyayyarsa a Twitter, wanda hakan ya ɗauki hankulan mutane sosai
  • Ta bayyana cewa ɗan uwanta a shekara huɗu da suka gabata ya gaya mata kuɗirinsa akan budurwar, ga shi yanzu ya cika

Wani matashi da ya tsunduma a cikin kogin ƙaunar wata budurwa bayan ya yi arba da ita a karon farko, ya samu nasarar aurenta.

Matashin ya haɗu da budurwar ne shekara huɗu da suka gabata, inda ba tare da ɓata lokaci ba ya gaya wa ƴar uwarsa cewa ya samu matar aure.

Matashi ya yi wuff da kyakkyawar budurwarsa
Matashin ya kamu da sonta lokacin da ya fara ganinta Hoto: @EGYPTlANA
Asali: Twitter

Burinsa na auren masoyiyar ta sa ya cika, inda aka sanya hotunan aurensu a Twitter.

Kara karanta wannan

Ana Cikin Yanayi Gwamnan PDP Ya Kori Ma'aikata 10,000? Gaskiya Ta Bayyana

Matashi ya faɗa soyayya, ya auri budurwarsa bayan shekara huɗu

Ƴar uwar matashin, Egyptiana, ta sanya hotunan aurensu, inda ta bayar da labarin soyayyar su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matashin ya gaya wa Egyptiana cewa idanuwansa na yin arba da budurwar kawai sai ya kamu da soyayyarta.

Ƴar uwarsa ta rubuta a Twitter cewa:

"Yau ɗan uwana yake auren babbar ƙawarsa. Shekara huɗu da suka gabata, lokacin da suka fara haɗuwa, ya tura min saƙo cewa ya kamu da sonta sannan zai zama miji a gareta. Ina matuƙar farin ciki sosai da waɗannan kyayawan ma'auratan."

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

OfficialBorbor ya rubuta:

"Ubangiji, ina kallon abin da ka ke yi wa sauran mutane."

@Enigmaiesh ya rubuta:

"Wannan shi ne abin da na ke nufi da na ce maza sun san cewa idan za su aureki lokacin da ku ke tare."

Kara karanta wannan

"Ba Amana": Budurwa Ta Rabu Da Matashin Da Ya Bude Mata Shago, Ta Koma Soyayya Da kwastoma

@legal__cocaine ya rubuta:

"Ina musu fatan su kasance tare har abada sannan su haifi yara masu yawa."

@muhofa_bridget ta rubuta:

"Kina da sauran wasu ƴan uwan? Ina ta ya ɗan uwanki murna.`

@Di_mi_nombre_ ya rubuta:

"Kyawawan ma'aurata! Ina ta ya su murna! Ina musu fatan alkhairi! Ina son Hotunan!"

Budurwa Ta Rabu Da Matashin Da Ya Yi Mata Hidima

A wani labarin na daban, wata budurwa ta watsawa matashin da ya yi mata hidima ƙasa a ido. Matashin ya buɗe mata shagon siyar da kayan sawa da kuɗinsa.

Sai dai, budurwar ba ta yi masa halacci ba, inda ta rabu da shi ta koma soyayya da kwastomanta, bayan ya samu karayar arziƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel