An Kwamushe Tsageru 15 Bisa Zargin Kai Farmaki Kan Bankuna a Jihar Akwa Ibom

An Kwamushe Tsageru 15 Bisa Zargin Kai Farmaki Kan Bankuna a Jihar Akwa Ibom

  • An kama wasu mutum 15 a jihar Akwa Ibom bisa zargin sun farmaki bankuna a wata karamar hukuma
  • Wasu masu zanga-zanga sun kai munanan hare-hare kan ma’aikatan banki a yankuna daban-daban na kasar nan
  • ‘Yan Najeriya an ci gaba da fuskantar kalubale kan yadda lamarin sabbin kudi ke zama matsala a gare su

Jihar Akwa Ibom - Akalla mutane 15 ne rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta sanar da kamawa a karamar hukumar Oron bisa zargin farmakar wasu bankunan jihar.

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Osiko McDon, inda ya ce a halin yanzu tsagerun na hannun jami’an tsaro.

Idan baku manta ba, akalla bankuna uku ne aka kone a wata kazamar zanga-zanga da ta barke a zagayen jihar a ranar Juma’ar da ta gabata, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kuna cutar da talakawa: Atiku ya caccaki CBN da Buhari kan sabuwar dokar kudi

Yadda aka kama masu hari kan bankuna
An Kwamushe Tsageru 15 Bisa Zargin Kai Farmaki Kan Bankuna a Jihar Akwa Ibom | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

A ranar Alhamis, an lahanta wasu mutane a turmutsutsun da ya faru a bakin CBN na birnin Uyo lokacin da jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka watsa taron masu zanga-zangar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mazauna garin sun dura ofishin CBN ne domin musayar tsoffin kudadensu a babban bankin bayan daina amfani da kudaden a cinikayya tsakanin ‘yan kasa.

Yadda lamarin ya faru da matakin da ‘yan sanda suka dauka

Da yake bayani game da kama tsagerun da suka lalata bankuna, McDon ya ce:

“Mun samu bayanan cewa an farmaki wasu bankuna a karamar hukuma Oron kuma ‘yan sanda sun fara daukar mataki.
“Da muke magana yanzu, an kama kalla mutum 15 da ke hannu a lamarin.
“Kwamishinan ‘yan sanda, Mr Olatoye Durosinmi ya bayyana rashin jin dadinsa game da lamarin kuma umarci jami’n yankin da lamarin ya faru na ‘yan sanda da ya tabbatar da ba a sake samun birkicewar doka da oda ba a yankin.”

Kara karanta wannan

An kassara 'yan bindiga, sojoji sun kashe kasurgumai bakwai a jiha Kaduna

A zauna lafiya, kiran ‘yan sanda ga jama’ar gari

Hakakazalika, kakakin na ‘yan sanda ya bayyana bukatar mazauna da su kasance masu bin doka da oda kana su guji lalata kadarori, Punch ta ruwaito.

Ya ce ‘yan sanda za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da an zauna lafiya a jihar Akwa Ibom da ma sauran jihohin Najeriya.

Har yanzu ana ci gaba da shan wahala game da sauyin kudi, shugaban kasa Buhari da kansa ya ba ‘yan kasa hakuri bisa wannan lamari da ke kara ta’azzara a cikin ‘yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel