Tinubu Ya Dauko Mutumin Buhari Ya Ba Shi Shugabancin Hukumar Kula da Almajirai

Tinubu Ya Dauko Mutumin Buhari Ya Ba Shi Shugabancin Hukumar Kula da Almajirai

  • Bola Ahmed Tinubu ya ba Birgediya Janar Lawal Ja’afar Isa mai ritaya shugabancin hukumar kula da sha’anin almajirai
  • Najeriya na fama da miliyoyin yaran da ba su zuwa makarantar zamani, saboda haka aka kafa masu wata hukuma ta musamman
  • Duk daga jihar ta Kano, Tijani Hashim Abbas ya zama mai ba shugaban Najeriya shawarwari a game da harkoki a kan masarautu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ba Birgediya Janar Lawal Ja’afar Isa mai ritaya mukami a gwamnatin tarayya.

Kamar yadda Ajuri Ngelale ya sanar a wani jawabi a yammacin Litinin, Lawal Ja’afar Isa zai rike hukumar kula da almajirai.

Bola Tinubu
Almajirai: Bola Tinubu ya ba Lawal Jafaru Isa mukami Hoto: @DOlusegun/Getty Images
Asali: UGC

Hadimin shugaban kasar ya bayyana tsohon gwamnan na jihar Kaduna zai jagoranci hukumar da aka kafa domin almajirai.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ba zai tafi da Sharada ba

Hakan yana nufin Hon. Sha’aban Sharada wanda aka nada daf da shugaba Muhammadu Buhari ya bar ofis ya sauka.

Sharada ya rasa kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya kuma bai yi nasara wajen zama gwamnan Kano a zaben 2023 ba.

Kafin ya bar karagar mulki, tsohon shugaban ya ba tsohon hadiminsa wannan matsayi da nufin magance matsalar almajirai.

Janar Jafaru Isa ya shigo gwamnati

Kamar yadda Olusegun Dada ya sanar a shafinsa a X, Janar Jafar Isa mai ritaya ya yi gwmanan soja daga 1993 zuwa 1996.

Tsohon sojan yana cikin wadanda aka kafa jam’iyyar CPC da su a 2010, kuma ya yi yunkurin zama gwamnan jihar Kano.

Tinubu ya ba Tijani Hashim mukami

Sanarwar ta ce Bola Tinubu ya nada Alhaji Tijani Hashim Abbas a matsayin mai ba shi shawara game da harkar masaratu.

Kara karanta wannan

Jita-jitar siyasa yayin da El-Rufai ya ziyarci tsohon Minista a Najeriya, an yada hotunan

Shugaban kasar yana sa rai Janar Isa da Sarkin Sudan za su taka rawar gani wajen magance matsalolin da ake fama da su.

Sharada ya sallama bayan fadi zabe

A can baya, rahoto ya zo cewa Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya fitar da jawabi, yana taya NNPP murnar nasara a zaben Kano.

‘Dan takaran Gwamnan na 2023 ya jinjinawa Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso da ADC da sha kahi a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng