Dakarun soji sun kubutar da mata 58 da mayakan Boko Haram suka tilastawa zaman dadiro da su (Hotuna)
- Rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwuiwar ‘yan agajin sa kai da ake kira “civilian JTF” sun yi nasarar kubutar da wasu mutane 148 daga hannun mayakan Boko Haram
- Dakarun sun kubutar da mutanen ne a jiya, Lahadi, yayin cigaba da atisayen kakkabe burbushin mayakan kungiyar Boko Haram da suka rage
- Yanzu haka hukumar soji ta mika mutanen hannun jami’an kula da sansanin ‘yan gudun hijira domin basu kulawa da matsuguni
A kokarin su na tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno, rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwuiwar ‘yan agajin sa kai da ake kira “civilian JTF” sun yi nasarar kubutar da wasu mutane 148 daga hannun mayakan Boko Haram ke tsare da su a kauyen Modu Kimeri dake karkashin karamar hukumar Bama.
Dakarun sun kubutar da mutanen ne a jiya, Lahadi, yayin cigaba da atisayen kakkabe burbushin mayakan kungiyar Boko Haram da suka rage a kauyunkan Modu Kimeri da Gulumba Gana bayan sun gudo daga yankin tekun Chadi da kuma wasu sassa dake iyakar jihar Borno ta arewa.
Daga cikin wadanda aka kubutar din akwai maza 15, mata 58 da kuma kananan yara 75. Mutanen sun shaidawa dakarun sojin cewar, mayakan na tilastawa matan saduwa das u duk lokacin da suka ga dama tare da yin amfani dam azan domin yi masu aiyuka masu wahala. Mata biyu daga cikin wadanda aka kubutar din na dauke da juna biyu.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga a jihar Zamfara na karbar haraji a hannun duk manomin dake son noma gonar sa
Yanzu haka hukumar soji ta mika mutanen hannun jami’an kula da sansanin ‘yan gudun hijira domin basu kulawa da matsuguni.
Kazalika dakarun sojin sun kara ragargazar wasu mayakan Boko Haram din tare da kwato makamai masu dumbin yawa a kauyukan sabon Gari – 1, Sabon Gari – 2, Sabon Gari – 3, Sabon Gari – 4, Nguzoduwa, Falla, Bulangala, Botori, da Bula Matawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng