Fasto Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga Tinubu Kan Sulhun Sheikh Gumi da 'Yan Bindiga

Fasto Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga Tinubu Kan Sulhun Sheikh Gumi da 'Yan Bindiga

  • Shahararren Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya tura sakon gargadi ga Shugaba Tinubu kan yin sulhu da Ahmed Gumi ya ce zai jagoranta
  • Elijah ya ce hatsari ne ba farar hula damar sulhu da 'yan bindiga inda ya ce ya kamata a binciki Gumi kan mu'amala da ya ke yi da su
  • Wannan na zuwa ne bayan Sheikh Gumi ya nuna a shirye ya ke domin sake jagorantar sulhu da ‘yan bindiga idan aka ba shi dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Babban Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya gargadi Gwamnatin Tarayya kan ba Sheikh Ahmed Gumi damar jagorantar sulhu da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bayan saukar da kai da amsa gayyatar Majalisa, Wike ya fadi gaskiyar lamarin rashin tsaro

Elijah ya na magana ne kan kokarin ceto dalban firamare 285 da aka sace a jihar Kaduna a makon da ya gabata.

Fasto ya gargadi Tinubu kan sulhu da Gumi ke neman jagoranta
'Yan bindiga: Fasto Elijah ya gargadi Tinubu a kan Sheikh Gumi Hoto: Elijah Ayodele, Sheikh Gumi, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Matsalar da sulhun Gumi zai jawo a Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa ya fitar, Osho Oluwatosin a yau Alhamis 14 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bai dace a ce farar hula ya na jagorantar sulhu da ‘yan ta’adda ba har sai dai idan ya na tare da su ko su na aiki tare.

Ya kara da cewa ba Gumi wannan dama zai kara yawan sace-sacen ne da biyan kudin fansa, cewar Tribune.

Shawarar da Faston ya ba Tinubu kan Gumi

Ayodele ya ba Shugaba Tinubu shawara da ya binciki Sheikh Gumi saboda sanin mu’amalarsa da ‘yan bindigan har ya sansu.

Faston ya ce ‘yan Najeriya ne suke da damar tallafawa jami’an tsaro domin tabbatar da kawo karshen matsalar tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Barazanar kisa: Gwamnan PDP a Arewa ya ba Remi Tinubu hakuri, ya daukar mata alkawari

Faston ya yi wannan gargadi ne yayin da Shehin malamin ya ce a shirye ya ke domin jagorantar sulhu da ‘yan bindiga, cewar Daily Post.

Gumi ya shirya jagorantar sulhu

A baya, mun ruwaito muku cewa Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana aniyarsa ta jagorantar sulhu da ‘yan bindiya.

Gumi ya ce wannan aikin alheri ne inda ya ce a shirye ya ke a kowane lokaci idan gwamnati ta ba shi damar haka domin dakile matsalar tsaro.

Ya kuma gargadi Shugaba Tinubu da kada ya yi kuskuren da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi a kokarin sulhun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.