Kar Ku Zabi Yan Siyasan Da Zasu Murkushe Yan Ta'adda, Sheikh Gumi

Kar Ku Zabi Yan Siyasan Da Zasu Murkushe Yan Ta'adda, Sheikh Gumi

  • Sheikh Dakta Ahmad Gumi yace arewa ba ta bukatar shugaban da zai murkushe 'yan bindiga baki ɗaya
  • Shahararren Malamin yace a halin yanzu ana bukatar shugaban da zai yi sulhu ne da 'yan fashin daji don zaman lafiya
  • Malamin dai ya yi kaurin suna wajen haddasa cece-kuce da magana kan yan ta'adda da suka hana zaman lafiya a arewa

Kaduna - Shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan dake yawan haddasa cece-kuce, Sheikh Ahmad Gumi, ya roki 'yan Arewa kar su zabi 'yan siyasar dake shirin murkushe 'yan bindigan jeji.

Jaridar PM News ta rahoto Malamin na cewa bai kamata a kashe 'yan bindigan jeji ba, kuma 'yan arewa na bukatar wanda zai yarda ya zauna da su a yi sulhu.

Sheikh Ahmad Gumi.
Kar Ku Zabi Yan Siyasan Da Zasu Murkushe Yan Ta'adda, Sheikh Gumi Hoto: Sheikh Ahmad Gumi
Asali: Facebook

Fitaccen Malamin Addinin mazaunin jihar Kaduna ya yi wannan furucin ne a ɗaya daga cikin karatuttukan da ya saba gudanarwa.

Kara karanta wannan

Bana son rigima: Buhari ya fadi abu 1 da zai yi bayan sauka daga mulki a 2023

A kalamansa, Sheikh Gumi ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Cikin 'yan takarar nan ina bin lafazinsu na ga lafazin waɗansu suna jiran wai kawai a basu mulki ne su kara makamai da za'a murkushe mayaƙanmu a cikin daji....mutanen mu a cikin daji."
"Alhali mu muna son a samu shugaban da zai zo a zauna da shi a fahimtar da shi, a kira mutanen nan a yi masu abinda ya kamata ai masu, don mu samu me? Zaman lafiya."

Duba bidiyon kalamansa anan

Sheikh Gumi ya jima tsawon shekaru yana kira da a yi sulhu da 'yan bindiga, waɗanda suka jefa mutane da yawa cikin matsin rayuwa ta hanyoyi da dama.

Malamin yace kauna da kishin kasa, jiha da mutane baki ɗaya ya sanya yake son a zauna da 'yan bindiga a yi sulhu.

A shekarar 2021, Shehin Malamin ya shawarci mazauna shiyyar arewa ta yamma da abun ya fi ƙamari da su gina alaka mai kyau da 'yan fashin jeji.

Kara karanta wannan

Matsanancin Halin Talaucin da za ka bar mu Ciki ya fi Wanda ka Tarar da mu, Kukah ga Buhari

A cewarsa mutane zasu iya kulla alaƙa mai tsafta da 'yan bindigan jeji ba tare da sun cutar da su ba.

Ba zan sake zura ido ana kashe mutanen Benuwai ba - Ortom

A wani labarin kuma Gwamna Ortom yace ba zai sake kame hannu yana kallo wasu tsageru na kashe mutanen jihar Benuwai ba

Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin bikin raba motoci da Babura ga Jami'an tsaron da gwamnatinsa ta kafa.

Yace Jira kawai yake shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince masa ya siyo bindigun AK47.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel