Gwamnan PDP Ya Bankaɗo Shirin Wasu Miyagu Na Kai Hare-Hare Makarantu da Sace Ɗalibai a Jiharsa
- Ademola Adeleke na jihar Osun ya banƙado wani shiri na kai sababbin hare-hare makarantu da gonakin al'umma a kauyukan jihar
- Gwamna Adeleke ya bayyana cewa ya samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu gurɓatattu na shirin kawo cikas a harkar noma da ilimi
- Ya kira taron majalisar tsaron jihar Osun kuma ya umarci makarantu su ɗauki matakan farko domin kare kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke ya ankarar da masu ruwa da tsaki kan yunkurin wasu gurɓatattu na kai hare-hare makarantu da gonakin al'umma a karkara a jihar Osun.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Olawale Rasheed, ya fitar jiya a Osogbo, babban birnin jihar.
Adeleke ya ce wasu bayanan sirri da aka tattara sun nuna cewa wasu gurɓatattu na shirya miyagu domin kai hari a kauyukan jihar, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ire-iren wadannan rahotanni marasa dadi na da matukar tayar da hankali da kuma haifar da babbar damuwa da fargaba a rayuwar al’ummar jihar Osun.
A cewarsa, gwamnatinsa ta shiga damuwa kan rahotonnnin leken asirin, inda ya ƙara da cewa masu ƙulla makircin na kokarin tarwatsa aikin gona ta hanyar sace mutane da kai hari kauyuka.
Gwamna Adeleke ya ƙara da cewa ana yunƙurin kai hare-hare makarantu da sace ɗalibai ne domin kawo cikas ga shirin tsaftace makarantu da gina ababen more rayuwa.
Wane mataki Gwamna Adeleke ya ɗauka?
Da yake bayyana matakan ya ɗauka domin daƙile kowane makirci, Gwamna Adeleke ya ce tuni ya kira taron majalisar tsaron jihar Osun domin tattauna batun
Haka nan kuma ya ce gwamnati ta umarci makarantu su ɗauki matakan kariya na farko domin tsare ɗaliban da ke karatu a cikinsu.
Adeleke ya kuma umarci kwamitin samar da abinci da ya gabatar da rahoton wucin gadi domin ba da damar daukar matakan kare gonaki da tabbatar da tsaron manoma yayin da damina ta gabato.
A rahoton Guardian, ya ce:
“An umarci ma’aikatar ilimi da dukkan hukumomin ilimi da su sake nazari kan matakan tsaro a makarantun jihar Osun bisa tsarin shirin Safe School Initiative."
Zaben Ondo: Kakakin majalisa ya shiga matsala
A wani labarin mun samu rahoton cewa Shugaban majalisar dokokin Ondo na fuskantar barazanar tsige shi daga muƙaminsa kan kalaman da ya yi na goyon bayan Gwamna.
Honorabul Olamide Oladiji ya yi ikirarin cewa ƴan majalisa 18 sun amince za su goyi bayan takarar gwamna mai-ci a inuwar APC mai mulki.
Asali: Legit.ng