Remi Tinubu Ta Yi Martani Kan Barazanar Kisan da Wani Malamin Addini Ya Yi Mata

Remi Tinubu Ta Yi Martani Kan Barazanar Kisan da Wani Malamin Addini Ya Yi Mata

  • Uwargidar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa yanzu ta kai shekarun da ba ta tsoron barin duniya
  • Remi Tinubu ta bayyana hakan ne yayin da take martani kan barazanar mutuwa da wani malamin addinin musulunci ya yi mata a baya
  • Raddin uwargidar kasar ya zo ne da ta kai ziyara a jihar Bauchi domin ƙaddamar da wasu muhimmin ayyuka da gwamnan jihar ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Oluremi Tinubu, uwargidar shugaban ƙasa Bola Tinubu, ta mayar da martani kan barazanar da wani malamin addini ya yi mata na fatan mutuwa a kwanakin baya.

A kwanakin baya ne dai wani faifan bidiyo ya bayyana na wani malamin addinin musulunci, inda ya ce uwargidan shugaban ƙasan ta cancanci barin duniya saboda addininta na Kirista.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fayyace gaskiya kan masu zargin Buhari ne ya lalata Najeriya

Remi Tinubu ta yi martani kan barazanar kisa
Remi Tinubu ta ce ba ta tsoron mutuwa Hoto: Senator Oluremi Tinubu
Asali: Facebook

Wane martani Remi Tinubu ta yi?

Sai dai, uwargidar shugaban ƙasan lokacin da take martani kan batun, ta yi nuni da cewa ta kai shekarun da bai kamata ta ji tsoron mutuwa ba, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana haka ne a wata ziyarar ban girma da ta kai wa Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwan Adamu kafin ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar.

A kalamanta:

"Ina so in gode wa mai girma (gwamnan Bauchi), ya ci gaba da ba ni tabbacin cewa ba ni da matsala a Bauchi amma ina so in ce na yi tsufan da ba zan ji tsoro ba.
Idan Allah ya ba ni sama da shekaru 60 a duniya, bai kamata in ji tsoron mutuwa ba.
"Na gode wa Allah da ka bani ƙwarin gwiwar zuwa. Najeriya tamu ce kuma wannan lokaci ne da ya kamata mu haɗa kai fiye da kowane lokaci.”

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya samu karramawa ta musamman a jihar Neja

Gwamna Bala ya ba Remi tabbacin kariya

Da yake mayar da martani, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya yi Allah-wadai da barazanar kisa da aka yi wa uwargidan shugaban ƙasar, inda ya bayyana hakan a matsayin wani babban abin kunya, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Mohammed ya nuna rashin jin daɗinsa, inda ya bayyana barazanar a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

Ya kuma tabbatar wa Remi Tinubu samun cikakken tsaron lafiyarta a jihar sannan ya yi alƙawarin ɗaukar matakin da ya dace kan malamin da ke da alhakin wannan barazana.

Shehu Sani ya kare Remi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi tofin Allah tsine kan barazanar kisa da wani malamin adɗinin musulunci ya yi wa Remi Tinubu.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa kalaman malamin ba abin yarda ba ne kuma kuskure ne mai girman gaske.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng