Tinubu Ya Ware Biliyan 150 Don Rage Radadi a Kanannan Hukumomi 774, an Fadi Ka’idar Cikewa

Tinubu Ya Ware Biliyan 150 Don Rage Radadi a Kanannan Hukumomi 774, an Fadi Ka’idar Cikewa

  • Gwamnatin Tarayya ta ware makudan kudade don rage wa kananan ‘yan kasuwa radadin cire tallafi a kasar
  • Gwamnatin ta kuma ware naira biliyan 75 don ‘yan kasuwar da kuma masana’antu a kasar da kudin ruwa kalilan
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan kasuwar magani kan wannan tallafi na Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta shirya raba naira dubu hamsin-hamsin ga kananan ‘yan kasuwa a fadin kasar.

Wannan shiri za a yi shi ne a dukkan kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar don rage wa jama’a radadin cire tallafin mai, Legit ta tattaro.

Tinubu ya ware biliyan 150 don rage wa 'yan Najeriya radadin cire tallafi
Tinubu ya ware wa 'yan Najeriya biliyan 150 na tallafi. Hoto: State House.
Asali: Facebook

Yaushe Tinubu ya sanar da kudaden tallafin?

Ministar masana’antu da kasuwanci, Doris Uzok-Anite ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa a Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu ya siya hannun jarin Atiku na $100m a kamfanin Intels? Fadar shugaban kasa ta yi magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Doris ta ce shirin kunshi tsarin shugaban kasa na rage radadin tallafi musamman ga kananan ‘yan kasuwa don bunkasa jarinsu.

Vanguard ta tattaro cewa masu son shiga tsarin za su samar da adireshin gdajensu da kuma na kasuwanci da sauran muhimman takardu.

Sanarwar ta ce:

“Gwamnatin Tarayya ta hannun ma’aikatar masana’antu da kasuwanci za su hada karfi da kungiyar kananan ‘yan kasuwa da ‘yan Majalisa da masu ruwa da tsaki.
“Wadanda ke da damar cin gajiyar za su bayar da adireshin wurin zamansu da na kasuwancinsu.
“Sauran muhimman abubuwan da ake bukata sun hada da asusun banki da lambar BVN da sauran muhimman takardu.”

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta kuma saka naira biliyan 75 ga kananan ‘yan kasuwa da wata biliyan 75 don masana’antu.

Ta ce kudin ruwa da za a karba ba zai wuce kashi tara kacal ba ne cikin 100 a cikin shekara guda.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir ya sanya yan fansho kuka yayin da ya cika musu alkwarin da ya dauka, ya koka

Martanin wani dan kasuwa kan tallafin

Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan kasuwar magani kan wannan tallafi na Tinubu.

Dan kasuwar mai suna Abubakar Umar Usman ya ce wannan mataki ya yi dai-dai inda ya yi fatan isa inda ya kamata.

Ya ce:

"Mu na maraba da kuma farin ciki bisa wannan kyakkyawan yunkuri na Gwamnatin Tarayya.
"Fatan dai Allah ya sa tallafin ya isa hannun wadanda su ka dace a tallafawa."

Ma’akata 5,000 za su rasa albashin Disamba

A wani labarin, Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya akalla dubu biyar ne za su rasa albashin watan Disamban da mu ke ciki.

Mafi yawan ma’akatan sun samu matsala ne a takardun daukarsu aiki da kuma na haihuwarsu wanda ya sha bamban da juna.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin matsin tattalin arziki tun bayan cire tallafin man fetur a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel